Abba Ibrahim Wada" />

Ban Ji Dadin Yadda Bayern Munchen Ta Kore Ni Ba, Cewar Kovac

Nico Kovac, mai koyarwa da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta kora, ya bayyana cewa bai ji dadin samun labarin korar da kungiyar ta yi ma sa ba duk da cewa sakamakon wasa ba ya kyau a ‘yan kwanakin nan.
Bayern Munich dai ta sallami kocinta, Niko Kobac bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Frankfurt da ci 5-1 a Bundesligar Jamus wasan karshen makon daya gabata.
Kobac ya bar Bayern Minich a mataki na hudu kan teburi, maki hudu kenan tsakaninta da Borussia Monchengladbach, wadda ke ta farko a saman teburi kuma a wannan satin kungiyar kungiyar zata buga kofin zamakrun turai.
Tsohon dan wasan tsakiyar Croatia mai shekara 48, Kobac ya fara jan ragamar kungiyar Bayern a watan Yulin shekarar 2018 kuma Kobac ya ya yi nasara a wasanni 45 cikin 65 da ya ja ragamar kungiyar, sai dai abin kunyar da ta yi shi ne karo na farko mafi muni a cikin shekara 10 a gasar Bundesliga.
Bayan wasan ne Kobac ya bayyana cewa ba shi da tabbas kan makomarsa a kungiyar inda yace ya san yadda harkar take, kuma ba ya jin ko dar saboda kashin da suka sha a wasan nasu na ranar Asabar.
Ya kara da cewa ra’ayinsa ba shi da wani amfani domin wadanda suke yanke hukunci su ne za’a tambaya game da halin da ake ciki sai dai a daren Lahadi kungiyar ta fitar da sanarwar cewa bazata cigaba da aiki tare da shiba.
Sai dai bayan sanarwar mai koyarwar, wanda ya taba bugawa kungiyar wasa lokacin da yana buga kwallo ya ce baiji dadin labarin korar tasa ba saboda yana kokarin saita kungiyar domin ta koma kamar baya.
Mataimakin kocin Bayern din Hansi Flick shi ne zai wakilci kungiyar a wasan da za ta fafata da Olympiacos a gasar Zakarun Turai ta Champions League ranar Laraba da kuma wanda za ta kece raini da Borussia Dortmund ranar Asabar.

Exit mobile version