Ban Ji Dadin Yadda Muka Doke Kasar Panama Ba -Southgate

Kocin tawagar kwallon kafar Ingila, Gareth Southgate ya ce, bai ji dadin yadda ‘yan wasansa suka taka leda a fafatawar da suka yi da Panama ba duk da cewa sun yi nasara da kwallaye 6-1.
Southgate ya yi amanna cewa, ‘yan wasan na Ingila za su iya nuna bajintar da ta fi wadda aka gani a yayin fafatawar ta ranar Lahadi a gasar cin kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Rasha.
Kocin ya kara da cewa, bai ji dadin yadda ‘yaran nasa suka fara wasan ba, kana bai ji dadin yadda suka ci kwallon karshe ba.
A yayin wasan dai, Hary Kane ya jefa kwallaye uku a ragar Panama, sai kuma John Stone da ya jefa kwallaye biyu, yayin da Jesse Lingard ya ci kwallo guda.
A ranar Alhamis mai zuwa ne Ingila za ta kece rani da Belgium, lamarin da zai bada damar sanin wanda zai jagoranci teburi a tsakanin kasashen biyu a rukuninsu na G.
Ingila ta samu nasara a kan Tunisia da kwallaye 2-1 a wasansu na farko, wasan da Southgate ya ce, ya fi jin dadinsa fiye da na Panama saboda yadda fafatawar ta zafafa.
A bangare guda, Radamel Falcao na Colombia ya jefe kwallonsa ta farko a gasar cin kofin duniya , yayin da kasarsa ta samu nasara akan Poland da ci 3-0, lamarin da ya haifar da cikas ga yunkurin Poland na kai wa zagayen gaba a gasar.
Bisa dukkan alamu dai, Colombia ta sake daura damara a wannan gasa bayan kashin da ta sha a hannun Japan da ci 2-1 a wasansu na farko a rukunin H yayinda ita kuwa Poland ta gaza samun nasara a wasanta na farko da Senegal wadda ta doke ta da ci 2-1.
Kasashen Japan da Senegal na da kwarin gwiwar samun gurbi a zagayen gaba na gasar bayan sun yi canjaras 2-2 a wasansu na jiya, lamarin da ya bai wa kowannensu damar samun maki hur-hudu.
Sai dai ga alama wasan na jiya bai yi wa Senegal dadi ba, domin kuwa Japan ta haramta ma ta darewa saman teburin rukuninsu na H da maki 6.

Exit mobile version