Daga Muhammad Maitela
Shekarar 2020 tana gab da zuwa karshe tare da barin dimbin tabon miyakun da yan Nijeriya su ka tsinci kansu a cikinta. Hausawa sun ce: shekara ba ta gadon shekara, ko shakka babu, ba ma fatan 2021 ta gaji wadda ta gabaceta- duba ga yadda aka fuskanci manyan jarabawowi a cikin wannan shekara mai karewa.
Annobar korona wadda ta kunno kai a farkon wannan shekara mai karewa, hadi da ta kidan kalangun matsin tattalin arzikin da ya kwankwashi madigar yan Nijeriya, sai uwa uba matsalar tabarbarewar tsaron Boko Haram, yan bindiga dadi da barayin shanu hadi da ta garkuwa da jama’a, wadanda su ne matsaloli ma fi muni da su ka kassara yanayin rayuwar dan Nijeriya a cikin shekaru sama da 10 da su ka gabata.
Al’amari ne mai matukar tayar da hankali tare da daure kai, ganin yadda wadannan hare-hare da farmaki ga yan kasa a kusan kowace ranar Allah- dangane da hakan ne, a wannan mukala ta mu ta ranar Lahadi, za mu yo tilawar wasu daga cikin hare-haren da yan Nijeriya ba za su manta dasu ba.
Wata majiyar tsaro ta bayyana yadda wadannan maharan sun farmaki kwambar motocin Mai Potiskum da misalin 11:00 na dare, wanda hakan ya yi sanadin rayukan dogarawan sa hudu.
Yan Nijeriya da dama sun bayyana alhini dangane da abinda ya faru ga Mai Potiskum tare da bayyana matukar bacin ran yadda rayukan yan kasa su ka zama arha warwas a hannun yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
- An Farmaki Tawagar Gwamna Zulum
Harin kwanton-bannar da wasu mahara su ka kai wa tawagar Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya jawo zazzafar muhawara a tsakanin yan Nijeriya, harin da ya jawo mutuwar wasu jami’an tsaro da ke raka gwamnan.
An kai wa Zulum hari a sa’ilin da yake ci gaba da gudanar da rangadin da yake yi tare da kokarin raba kayan abinci da masarufi domin tallafa wa al’ummar yankunan da matsalar tsaro ta tagayyara a jihar, shirin da ya fara tun a cikin watan Yuli.
Gwamna Zulum ya shirya kai irin wannan ziyarar zuwa garin Baga a ranar Laraba, wanda muhimmin gari ne kuma sananne a sana’ar kamun kifi a kahon yankin Tabkin Chadi, yankin da ya sha fama tare da kasancewa karkashin mamayar mayakan kungiyar Boko Haram a shekarun baya, kafin daga bisani sojojin Nijeriya su sake yanto shi, kana da ikirarin gwamnati kan cewa babu wani bangaren Nijeriya a hannun mayakan.
- Harin Masallacin Jummu’ar Kauyen Maru
Daya daga cikin munanan hare-haren da su ka taba zuciyar Nijeriya shi ne farmakin da wasu yan bindiga su ma kai a ranar Jummu’ar 20 ga watan Nuwamban 2020. Wannan hattsabibanci na yan ta’addan da suka addabi kasar nan ya kai inda ya kai, wanda su ka kutsa har masallacin kauyen Dutsen Gari da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda su ka halaka kimanin masallata biyar tare da garkuwa da sama da mutum 30- a lokacin da ake gudanar da sallar jummu’a!
Yayin da shi kuma mai magana da yawon rundunar yan-sandan Nijeriya a jihar Zamfara, Mohammed Shehu ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP), “Yan bindiga dadi sun kashe masallata biyar da garkuwa da 18 ciki har da limamin masallacin, a lokacin da suke sallar jummu’a.”
- Garkuwa Da Jami’an Yan-sanda 12
A tsakiyar watan Nuwamban 2020 wasu yan bindiga dadi da ke garkuwa da mutane ne su ka yi awon gaba da mantan jami’an yan-sandan Nijeriya har 12, wadanda su ka taso takanas ta Kano daga jihar Borno zuwa Zamfara domin gudanar da aiki na musamman na magance matsalar tasaron da ta addabi yankin- kamar yadda ofishin mai magana da yawon rundunar yan-sanda ta Nijeriya, Frank Mba ya tabbatar.
‘Yan bidigar sun yi wa ayarin yan-sandan ma su mukamin ASP kwanton-bauna a kan hanyar Katsina zuwa Zamfara, wannan labarin ya kara daga hankulan yan Nijeriya tare da bayyana halin kaicho da kasar wanda hatta jami’an tsaron Nijeriya matsalar tabarbarewar tsoro ta fara basu tsoro.
- Harin Auno:
Daya daga cikin manyan hare-haren da ke ci gaba da zama a zukatan yan Nijeriya shi ne mummunan farmakin da yan kungiyar Boko Haram su ka kai a garin Auno, kauyen da ke kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, wanda ya ci rayukan sama da mutum 30 a daren wata Lahadin cikin Fabarairun 2020.
Baya ga karin wasu da su ka samu raunuka, haka kuma yan ta’addan sun kona motoci sama da 18; a ciki har da tireloli dauke da kayan abinci da na masarufi. Sannan da yadda wasu rahotanni su ka nuna cewa maharan sun yi garkuwa da wasu fasinjojin da ke dakon gari ya waye su shiga birnin Maiduguri a kauyen.
- Harin Zabarmari
Shima wannan hari ne wanda yan Nijeriya ba su zaton aukuwar sa, kana da yanayin da maharan su ka aiwatar da shi a kauyen Zabarmari a karamar hukumar Jere a jihar Borno wanda aka yi wa manoman shinkafa sama da 43 yankan rago a farkon karshen watan Dosamban 2020.
- Garkuwa da daliban makarantar Kankara
Kwatsam kuma, sai ga wani mummunan labari sabo fil a makon da ya gabata; a tsakiyar watan Disamban 2020, wanda ya nuna yadda wasu mahara suka farmaki makarantar kwana dake garin Kankara ta jihar Katsina tare da yin awon gaba da daruruwan daliban makarantar maza. Yayin da wannan aika-aikar ta kara ankarar da yan Nijeriya cewa fa har yanzu da sauran rina a kaba a mafarkin da suke yi a wannan dogon baccin da suke yi.
Wanda daga bisani gwamnatin jihar Katsina ta bayyana kubutar da yaran. Amma dai wannan al’amari ne da zai ci gaba da yin tasiri a zukatan yan Nijeriya.