Daga Abba Ibrahim Wada
Kociyan Manchester united, Jose Mourinho ya bayyana cewa har yanzu bai san lokacin da yan wasan ƙungiyar, Paul Pogba da Maroune Fellaini zasu dawo daga jinyar da suke ba.
Ɗan wasa Pogba dai yatafi ciwo tun watan daya gabata a wasan zakarun turai da ƙungiyar ta fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Basel a wasan sati na farko na gasar.
Sai dai a kwanakin baya Pogba ya bayyana cewa yana dab da dawowa bayan ya saka wani fefen bidiyo a shafinsa na twitter.
Ya cigaba da cewa, idan ana buƙatar lokacin dawowar Fellaini da Pogba sai dai ace a tambayi likitan ƙungiyar domin shine yake kula da lafiyar yan wasan ƙungiyar.
Sannan yace yasan dai cewa Eric Bailly yana kan hanyar dawowa fili amma bai san lokacin dawowar pogba da fellaini ba.
Pogba dai bai bugawa united wasanni 7 ba tun lokacin da yaji ciwo sai dai rahotanni sun bayyana cewa yana gab da dawowa filin wasa.