Connect with us

RAHOTANNI

Ban TaBa Ganin Sana’a Mai Albarka Kamar Sana’ar Kasa Ba

Published

on

Sana’ar saye da sayar da kasa, fili ko gida da makamantansu, sana’a ce mai dadadden tarihi, sai dai a lokuta da yawa a kan yi wa masu wannan sana’ar ganin marigimta ko ma’abota cin amana. To ko haka abin yake, ko kuma wasu ne ke Bata wasu? Muhammad Umar Bama, sanannen dillalin filaye da gidaje ne da makamantan hakan a nan garin Kaduna. Ya fayyace mana komai da ke cikin wannan sana’ar, dadin ta da kuma wahalarta da abin duk da ke kunshe a cikin ta. Sun zanta ne da wakilinmu, Umar A Hunkuyi, a ofishinsa da ke unguwar Danmani, Rigasa, Kaduna.

A sha karatu lafiya:

Masu karatunmu za su so ka gabatar masu da kanka?

Sunana Muhammad Umar Bama, Shugaban kamfanin harkan saye da sayar da filaye da gidaje na, Kanuri Estate Agency and Property Manegement.

 

Kamar ya kuke ganin yadda sana’ar taku ke tafiya a irin wannan lokacin?

A gaskiya, sana’ar kasa kamar a nan Kaduna, yadda abin ke tafiya a halin yanzun, kamar ba zai taimaki su masu yin sana’ar ba. Kasantuwar yanda ake yin abin babu tsari, ita kuwa sana’a duka, tana da bukatar tsari na shugabanci da jagorori, wanda a halin yanzun a nan Kaduna babu ko guda daya. To in kuwa ana zaune ne a haka kara zube, ba wani abin da zai yi tasiri, wannan kuwa shi ya sanya zaka ga a kullum matsalolinta yana fin alherinta yawa, wannan ne kuma dalilin da ya sanya zaka ji ana ta yin korafi a kan su dillalan.

 

To Mene ne mafita?

Mafita ita ce, kamar yadda yawancin wadanda suke kamar na gaba a cikin wannan sana’ar,wacce ke da mahimmanci a kasa, duk da sun san wannan sana’a ce mai jigo, amma sun nu na ba su damu da wannan abin ba, in ana maganan tattalin arzikin kasa, wannan sana’ar tana daga cikin abin da ke haBaka tattalin arzikin kasa, amma su masu kamar shugabantan lamarin sun yi biris da shi. Ba su tsaftace sana’ar ba, ta yanda za su sanya tilas gurBatattun dillalai wadanda yawanci da su ake kashe-mu-raba, su gyara halayen su. Don haka matukar ana son sana’ar ta yi tasiri ta inganta, tilas ne sai shugabanni sun shiga ciki.

 

Sau da yawa ana kokawa da masu wannan sana’ar kan irin yanda suke gudanar da harkokin su, ana ma da yawa daga cikin su ganin marasa gaskiya, me zaka ce a kan hakan?

Duk da shike ni ina da ja, a kan abin da yake kawo rashin gaskiyan, domin yawanci rashin gaskiyan yana a tsakanin mai sayarwa ne da kuma mai kaya, domin mutum ne zai zo yace maka, ga wuri naka sayar mani da shi Naira milyan 10, in ka sayar hakan, ni zan baka kashi biyar na kudin, amma kuma da zaran ka sayar ka zo ma shi da kudin sai ka ga yana neman ya dauki kashi biyu ko ma daya na kudin yaba ka, wanda kuwa canza tunanin dillali a irin wannan lokacin wanda kuma ya shafi magana ne na kudi, abu ne mai hadari. Wanda in har a ce an yi gaskiya, to yana da wahala ka ga dillali ya nemi ya yi zalunci. Sannan kuma wani lokacin kaine zaka janyo mutum domin ya zo shi ma ya ci arziki, to amma sai ka ga yana kokarin ya nu na maka ya fi ka kwakwalwa, wanda kuwa hakan ba mai yiwuwa ne ba.

 

Wasu na ganin wannan ba sana’a ce da sai an koya ba, da zaran mutum ya sami sarari ne kawai sai ya fada a cikin ta, ko hakan ne?

Wannan ba gaskiya ne ba, wannan sana’ar ana koyon ta ne, tun farko wannan sana’ar tana da bukatar a san wane ne ubangidanka, shi ma ubangidan naka shi waye ne, yana kuma yin wannan sana’ar na shi da tsafta, kuma wace irin kwarewa yake da ita a wannan sana’ar? Domin sai ka shigo ba tare da ka koya ba, sai aka baka gidan marayu aka ce ka kiyasta ma shi kudi, in baka iya ba, a nan wane labari zaka bayar, a nan gidan milyan 10, kana iya kiyasta shi a milyan 6, ko na milyan 3 ka kiyasta shi a milyan 6, to me ka yi a nan? Don haka tilas ne ka yi biyayya ka koya ka kuma iya. Kwanan nan nayi kiyasin wasu gidaje sun kai 50, kuma ba wanda aka sami wani ba daidai ba a cikin su, wanda da ban iya ba, yazan yi har a yarda a raba gado a kan kiyasin nawa? Don haka sai ka iya, akwai bukatar ka koya, bayan ma ka koye ta, ka kuma koyi yanda ake mu’amala da masu saye da kuma masu sayarwa.

 

Kamar wadanne matakai ne ake bi wajen shigan na ta?

Farko dai ka duba wanda zaka yi tarayya da shi domin ku yi wannan harkan, wane ne shi? Wanda ana ganin ka a tare da shi, kana kuma hakuri da abin da yake baka, yau ka samu gobe ka ci hakuri, kana dai bin shi kana koyon yanda harkan ke tafiya. To duk ranar da yace maka, wane na ga abubuwa sun yi nisa, ga jama’a sun yi maka yawa, ni kuma ga dan abin da nake baka, to ko za a dan nemi wane waje ne kai ma ka kama? Wanda yawanci ba sa jiran hakan, kawai da zaran mutum yana ganin shi ma ya dan yi ido kawai sai ya je ya kama waje, wannan shi ya sanya abin yake tafiya babu tsari.Ake ta fama, yau ka ji an damfari wannan, gobe ka ji an damfari wancan, shi ma kanshi dillalin wasu ‘yan 419 su zo su dankara ma shi filin da ba na gaskiya ba. Wanda duk wannan rashin tsari ne ke kawo shi.

 

To rajista ake yi kafin a shiga ko ya abin yake?

Kwarai kuwa, yau in ka zo wannan ofishin nawa, za mu nu na maka ka’idojin mu da sharuddan mu, ba cin amana, baka barin wannan ofishin ka koma wancan ka je kana ciniki, sai dai duk cinikin da ka kawo, sai ka zo nan ofis a yi ciniki, ko mutane nawa ne, sai ka zo nan ofishin da kake zaune a yi ciniki a rubuta takarda a bayar. Kar kuma ka je ka sayar da kayan da ba naka ba, ba kuma yin fada da abokanan ciniki, komai abokin ciniki ya gaya maka tilas ne ka zama mai hakuri, duk wadannan suna daga cikin tsare-tsaren mu.

 

Yanzun shekarunka nawa ne kana yin wannan sana’ar?

Ni na kai shekaru 25 a wannan sana’ar.

 

A nan Kaduna ka fara ko ka yi a wani wajen?

A’a, a Abuja na fara.

 

Ka yi rajista da gwamnati ne ko ya abin yake?

Ka ga dai ina da rajista da, Cooperate Affairs, ina kuma da sanayya da EFCC, wanda sun ba ni takardan shaida, sun kuma ba ni adadin kudin da zan sanar masu, da dai makamantan hakan.

 

A karshe wane kira ka ke da shi ga ‘yan’uwanka masu yin wannan sana’ar?

Wannan sana’a ce mai albarka, ni tun da nake ban taBa ganin sana’a mai albarka kamar sana’ar cinikin kasaba, kuma babu sana’ar da take da fitina, kamar wannan sana’ar ta mu, wanda kuma yawanci mune muke kirkiran ma kanmu wannan fitinar, domin mun kasa gane na kwarai da kuma Batagarin da suke a cikin mu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: