Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce bai taba tunanin zai koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ba domin koyar da ‘yan wasan kungiyar.
Mista Wenger yayi wannan magana ne kwanaki kadan bayan da tsohon shugaban gudanarwar Manchester United, Martin Edward ya bayyana cewa wenger ya kusa komawa united a shekarun baya.
Kamar yadda Martin Edward ya rubuta a littafinsa na tarihin rayuwarsa ya ce, Arsene Wenger shi ne zabinsa a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon kocin kungiyar Sir Aled Ferguson a lokacin da Aled din yayi niyyar yin ritaya a shekara ta 2001 kafin daga baya ya canza shawara.
Edward ya cigaba da cewa sun zauna da Wenger a gidansa da ke birnin London akanmaganar komawa United din kuma ya nuna sha’awarsa akan hakan.
Sai dai wenger ya karyata maganar inda yace ya na girmama kungiyarsa ta Arsenal sannan yace Manchester United babbar kungiya ce amma bai taba tunanin komawa kungiyar ba.