Ban Taba Yin Kama Da Talaka Ba A Fim – Jarumar Indiya Kajal

Kajol

Jarumar Indiya mai suna Kajol a cikin fim din ‘Koffee’ na Karan ta bayyana cewa, ba ta taba yin kama da talaka ba a cikin shirin fim, ko da kuwa ta saka kayan gargajiya da talakawa suke sakawa.

Tana wannan tsokacin ne a game da Fim din ‘Tribhanga’ da ta yi a shekarar 2014, wanda shi ne fim na karshe da jaruma Kajol ta yi da aka saki a farkon wannan shekarar. Lokacin da ta bar shirin fim a shekarar 2014, an tambaye ta ko za ta sake dawowa shirin fim.

An dai yi mata wannan tambayan ne lokacin fim din ‘Koffee’ wanda Karan ya shirya, Karan Johar ya tambayi Kajol ko tana da ra’ayin sake dawowa shirin fim a nan gaba. Ya bayyana cewa, ya kalubalance ta a kan rawar da ta taka.

Ta amince ba ta ji dadin bangaren da aka saka ta ba, inda ta bayyana cewa, “ina tsammanin a duk shekara ina fitowa a matsayin mai kudi. Ban yi kama da talaka ba, a duk abin da nake yi, ko da na saka kayan gargajiya da takawa suke sakawa, ina kallon kaina ni ba talaka ba ce.”

Karan ya ce, “ina tunanin Kajol ta yi kuskure. Kina daga ra’ayinki na kashin kai, saboda na ce kin fito a matsayin talaka a wasu tsirarun fina-finai.”

Nan take Kajol ta mayar da martani a fim din ‘Dilwale’ wanda take kalubalantar Shah Rukh Khan.

Jarumar ta yi magana a kan makomanta a wata hira da aka yi da ita a farkon wannan shekarar. Ta ce, “na yi matukar sa’a, wannan yana tattare ne da yadda kake son kanka da kuma yadda ka yarda da kanka. Ina tunanin hakan yana kasancewa ne kan yadda ka girmama kanka a wajen aikinka. Ban tunanin hakan zai yiwu idan ya kasance ko da yaushe ina zaune a gida. Bana yin hakan. Ina yawan aikatuwa da kara kwazo da tunanin zan samu ci gaba fiya da yadda nake a baya.”

Exit mobile version