Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, ya kamata a kowane lokaci Ministoci, Hukumomi da dukkan Shugabannin sassan su dinga nuna girmamawa ga Majalisar Dokokin kasa, shugabanninta da mambobinta.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata, lokacin da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Ibrahim Lawan da Shugaban Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila suka kawo masa ziyara a Fadar sa da ke Abuja.
Shugaban, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun Mataimakin sa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya sake jaddada matukar girmamawar da yake wa Majalisar Dokokin kasar.
Ya ci gaba da cewa, ba zai dauki rashin girmamawa daga gurin wani memban ofishin zartarwa ga majalisar ba. A yayin tattaunawar tasu, sun bayyana abubuwan da suka faru kwanan nan a Majalisar. Tattaunawar tasu wanda ya dauki kusan tsawan awa daya, domin sun tattauna akan batutuwan da suka shafi mahimmancin kasa musamman rawar da majalisar dokokin ke taka wa wajen tallafawa da inganta rayuwar mutanen Nijeriya.
A ranar 30 ga watan Yuni ne, Karamin Ministan a Ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, Festus Keyamo ya samu sabani da wakilan Majalisar tarayya, lokacin da ya bayyana a gaban kwamitocin hadin gwiwar Majalisar Dokoki ta kasa kan samar wa matasa 774,000 aikin yi a karkashin Shirin Ayyukan Jama’a na Musamman (SPW).
A wannan lokacin ne jayayya da fadan kalmomi masu zafi suka shiga tsakanin Ministan da ‘yan majalisar. Don haka ne, majalisar ta ba da sanarwar dakatar da shirin.
Amma bayan haka ne, Shugaba Buhari, a ranar Talata, ya bayyana cewa, ya ba Ministan goyon baya ta hanyar ba shi damar ci gaba da aikin, duk da dakatarwar da Majalisar ta yi.