Abdullahi Muhammad Sheka" />

Bana Masu Layya Sun Gwammace Sayen Rakuma Maimakon Shanu A Kano

Ranar Talata ce ke zaman Ranar da al’ummar Musulmi a fadin Duniya zasu gudanar da bukukuwan Salla Babba, Kamar Yadda aka sani wannan Sallace wadda al’ummar Musulmi ke gudanar da Layya domin samun Lada.  Kamar kowacce Shekara idan irin wannan lokaci ya gabato Kasuwar Dabbobi ce ke zaman wuraren da ke daukar Hankali. Musamman ganin yadda ake tururuwa da dabbobi wanda suka hada  da Shanu, Raguna, Rakuma da sauran dabbobin da shari’a ta aminta da yin layya dasu.

Ire iren dabbobin da ake layya dasu, Rago ne ke sahun gaba wajen farin jini wadda kuma jama’a suka fi mayar da hankali wajen sayen sa domin yin layya dashi, amma a wannan shekara lamarin nema yake ya sauya, musamman duba da matsin tattalin arziki da Duniya ke fuskanta ba wai kasarnan ba kadai. Wannan tasa a zagayen da Jaridar Leadership Ayau Asabar ta yi na ganin kwakwaf domin duba  halin da Kasuwar dabbobin ke gudana ta sauka a Kasuwar Abbatuwa.

Kasuwar Abbatuwa itace Kasuwar dabbobi mai ci yau da kullum a Jihar Kano, Musamman Kasancewar ta nan babbar mayankan dabbobi ta Kano ta ke, kuma a wannan Kasuwa ake kawo manyan dabbobi da kanana, ga kuma Rakuma da ake shigowa dasu daga makwabtan Kasar nan. Abubuwa guda biyu ne su kafi daukar Hankalin Jaridar Leadership Ayau Asabar, wanda suka hada da yadda masu Karamin Karfi suka fi karkata bangaren sayen ‘yan Kananan raguna da tumaki wadda akafi sani da Kafi zuru. Ya yinda Masu hannu da shuni kuma a wannan shekara suka koma sayen Rakuna a madadin sayen manyan Shanu da suka saba saye a shekarun da suka gabata.

Malam Rabi’u Dan Uwa karamin ma’aikaci ne wanda Jaridar Leadership Ayau ta iske yana cinikin wani Kafi zuru, inda wakilinmu ya matsa kusa dashi tare da jefa masa tmbayar cewa shin baya ganin kamar wannan ragon ya yi kankanta? Sai ya amsa da cewa halin da ake ciki ne ya tilasta mu sayen irin wadannan dabbobin domin dai a samu a yanka kar yara suyi ta zare ido. Ya ce sayen kafi Zurun ma sai wanda ya daure inji Malam Rabiu.

A Bangaren masayar Rakuma kuwa wani dattijo da ya bukaci mu sakaya sunansa ya bayyanawa Jaridar Leadership Ayau Asabar cewa gaskiya Rakuma sunfi Shanu sauki kuma sunfi su Nama, yace kaga wannan Rakumin da na saya Naira dubu 120 ya fi San Naira Dubu 150 kuma yafi shi Nama, da aka tambayeshi shin ko ina batun taurin Naman da ake cewa Rakumi na dashi?, Sai ya amsa da cewar Ko kadan naman Rakumi bashi da wani tauri, kuma yanzu haka ai duk cinye naman Rakumin ake a cikin gidaje ba a ma san naman Rakumi ba ne.

Yanzu haka dai kamar yadda Jaridar Leadership Ayau Asabar ta ganewa idonta yadda Kasuwannin dabbobi a Kano suka fara cikar kwari, sannan kuma ga kayan suya ko ina an baje kolinsu domin masu bukatar saya,  sai kuma daya tsarin na watanda wanda Jama’a kanyi karo karo domin sayen Sa ko rago domin yankawa a raba kowa ya dau nasa kason domin kaiwa a dan salalawa yara domin sawa abakin salati, dukkan lunguna da sakona tuni ya dau harami da irin wadannan kayan bukata. Fatanmu Shi ne Allah sa a yi sallah Lafiya.

 

 

 

Exit mobile version