Abba Ibrahim Wada" />

Bana Tunanin Griezman Zai Bar Atletico Madrid, Cewar Kociyan kungiyar

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Diego Simeone ya bayyana cewa ko a zuciyarsa baya kawo cewa dan wasan kungiyar Antoine Griezman zai bar kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
A kwanakin baya kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kusa siyan dan wasan sai dai daga baya dan wasan da kansa yace bashi da niyyar barin kungiyarsa kuma yana son cigaba da zama domin kafa tarihi.
Sai dai wasu rahotanni a kwanakin baya sun bayyana cewa dan wasan ya fara dana sanin rashin komawa Barcelona a shekarar data gabata kuma aka bayyana cewa yanzu yana shirin bawa Barcelona hakuri domin su koma su sake nemansa.
“Gaba daya bana tunanin cewa Griezman zai bar Atletico saboda haka bana damuwa da jita jitar da ake ya dawa cewa yana son tafiya kuma shine kyaftin dinmu saboda haka bai nuna mana alamar komai ba ta yana son tafiya” in ji Simeone.
Griezman dai a wannan kakar ya zura kwallaye 18 cikin wasanni 39 daya bugawa kungiyarsa ta Atletico Madrid kuma a shekarar data gabata ya taimakawa kasarsa ta Faransa ta lashe kofin duniyar da kasar Rasha ta karbi bakunci.
kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ma dai tana zawarcin dan wasan wanda tun lokacin tsohon kociyan kungiyar, Jose Mourinho ya nemi da kungiyar ta siyo dan wasan amma dan wasan yace bazai bar inda yake ba.

Exit mobile version