Bangaren Lantarki Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 20.5 Saboda Karancin Gas

Lantarki

Bangaren wutar lantarki a Nijeriya ya tafka asarar harajin naira biliyan 20.5 a tsakanin ranar 1 ga watan Junairu zuwa ranar 22 ga watan Junairun shekarar 2021, sakamakon korabi da ake samu na karancin rarraba wutar lantarki. Daga rahoton da ma’aikatar wutar lantarki ta fitar ya nuna asarar da aka samu a bangaren na naira biliyan 20.5 a farkon makanni uku na wannan shekarar. An dai bayyana cewa, a tsakanin wannan lokacin da kididdigar, an samu karancin rarraba wutar lantarkin wanda hakan ya shafi tafka asara a harajin da ake samu. An dai samu wannan babban matsalace sakamakon karancin gas na rarraba wutar lantarki da kuma karancin ababen more rayuwa. Bincike daga ma’aikatar ya nuna cewa, a wannan lokaci an rarraba wutar lantarki ne wanda ya kai megawatt 4,505 kadai a cikin awa guda.

Shugaban gudanar da harkokin kasuwancin na kamfanin da ke samar da wutar lantarki a Nijeriya, Edmund Eje ya bayyana cewa, an samu zaftarewar haraji mai yawan gaske a cikin kasuwancin wutar lantarki. Eje ya bayyana hakan ne ta taron da ya gudana ta faifan hoton bidiyo domin tattauna hanyoyin inganta wutar lantarki a cikin kasar nan.

Ya ce, “an fara samun baban gibi a kasuwancin wutar lantarki a Nijeriya. Dole ne kamfanonin rarraba wutar lantarki su rage yawan lodi a wannan wata. Ta haka ne za a rage yawan dauke wutar lantarki.

“Idan aka samu nasarar rage yawan dauke wutar lantarki, ta haka ne kamfanonin samar da wutar lantarkin za su sami kudade masu yawa a bangarensu.

“A yanzu haka akwai sababbin kayayyakin kimiyya da za su zo wanda hakan zai bayar da damar farfado da wutar lantarki,” in ji shi.

Exit mobile version