Bangaren sauka na kumbon Shenzhou-21, dauke da ‘yan sama jannatin na kumbon Shenzhou-20 wato Chen Dong, da Chen Zhongrui, da Wang Jie ya sauka doron duniya cikin nasara.
Sundukin ya sauka ne a yau Jumma’a a yankin Dongfeng na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai, dake arewacin kasar Sin, kamar dai yadda aka tsara.
Rahotanni na cewa, dukkanin ‘yan sama jannatin suna cikin koshin lafiya. Kafin dawowarsu doron duniya sun shafe kwanaki 204 a sararin samaniya, lokaci mafi tsayi da ‘yan sama jannatin kasar Sin suka taba shafewa a samaniya, kamar dai yadda hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati ta Sin ko CMSA ta sanar.
Kwamandan ‘yan sama jannatin Chen Dong, shi ne ya fara fitowa daga sundukin bayan saukarsa doron kasa. Kawo yanzu, Chen ne dan sama jannatin kasar Sin daya tilo da ya shafe jimillar sama da kwanaki 400 a sararin samaniya. (Saminu Alhassan)













