Bangaren Shari’a A Nasarawa Ya Dawo Da Mutanen Da Ya Dakatar

Bangaren shari’a a jihar Nasarawa, ya dawo da kimanin mutum 20 da ya dakatar da su tsawon watanni goma sha daya  sakamakon keta hurumin shari’a.Wadanda aka dakatar din dai sun gudanar da zanga-zanga ne zuwa cikin kotun a yayin da ake gudanar da shari’a.
Masu zanga-zangar sun gudanar da zangaizangar ce domin neman hakkokin su da suke zargin ana hada baki da Gwamnati a handame.
Tare da nunar da cewa an tauye masu hakkokin su na aiki, sannan babu batun karin matsayi a wajen aiki na tsawon shekaru, haka-zalika suna zargin babban Jojin da nuna bambanci a tsakanin Ma’aikatan.
Wannan ya sanya suka gudanar da zanga-zaga zuwa cikin Babban Kotu a lokacin da Babban Jojin yake gabatar da shari’a, zanga-zangar ta sanya ala tilas ya janye shari’ar ya koma ofishin sa. An dai gudanar da zanga-zangar ne a watan shadaya ta shekarar dubu biyu da sha takwas.
A ranar 16 ga watan nan ne masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a na jihar karkashin Babban Jojin jihar, mai shari’a Sulaiman Dikko, suka gudanar da zama na karshe dangane da matsalolin wadanda aka dakatar.
Sakamakon zaman da aka turawa manema labarai ya nuna cimma matsayar dawo da wadanda aka dakatar din tare da hukunta su ta matsayin rage masu girma tare da kuma cimma matsayin tun da ba su yi aiki a tsawon watannin na baya ba to babu batun biyan albashin watannin.
Duk da cewa Kwamitin ya ce ya yi masu sassauci saboda su karankansu sun san sun aikata babban laifin da ya cancanci a daure su a gidan kaso.
Sannan Babban Jojin ya soke kudaden Ma’aikatan da ake cirewa kungiyar ta bangaren shari’a na duk karshen wata.
A don haka, za su raba takardan sakamakon zaman ga mahukunta a jihar da ma masu fada a ji a bangaren shari’a.
Wadanda aka dakatar kuma aka dawo da su bakin aikin sun hada da:
1. Musa Jimoh Alonge
2. Solomon Iyigulu
3. Sunday Daniel
4. Jonathan Abe
5. Nao’mi Zekpo
6. Anna Ambi Engom
7. Joseph Abugu
8. Yakubu Hussain
9. Muhammed Liman Usman
10. Shuaibu I. Loko
11. Abubakar Gambo Adamu
12.Sarah A.Awotu
13. Manji Simon
14. Yakubu Abubakar
15. John Ogu Abu
16. Kokona Na’omi
17. Solomon Osakudu
18. Ibrahim Loko
19. Talatu Echem
20. Haruna Ibrahim

Exit mobile version