Bangarorin PDP A Yobe Sun Yi Baran-Baran Da Juna

Wata sabuwar takaddama ta barke a tsakanin kusoshin jam’iyyar PDP a jihar Yobe, yanayin da yaya jawo yiwa juna kallon hadarin kaji, inda kowanne bangare ya shan alwashin raba gari da juna.

Dakta Yerima Lawan Ngama (Matawallen Bade), kuma tsohon karamin ministan kudi kana kuma jigo a jam’iyyar a jihar Yobe ya bayyana wa manema labarai- bayan kammala wani taron kusoshin ta, a Damaturu kan cewa PDP ta na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida.

Lawan Ngama ya ce “wannan jam’iyya ta  PDP ta dade a cikin rikici wanda ya fara tun bayan Kafuwar ta a shekarar 1998 da karbuwar ta a jihar Yobe, duk da nasarar da ta samu a zaben 1998- sa’ilin da jam’iyyar PDP ta lashe kananan hukumomi 10 daga cikin 17 da ake dasu a jihar Yobe. “

“Sai dai a cikin rashin sa’a, tun daga wancan lokacin jam’iyyar ta fada gararari da takon-saka tare da rikici a tsakanin jiga-jigan ta, har zuwa yau. Rikicin da yake gudana ta dalilin bin son zuciyar  wasu tsirarun shugabanin ta a matakin jiha da tarayya.”

“A tarihin wannan rikici, wanda ya haifar da yiwa jam’iyyar zagon kasa tare da faduwa kasa warwas, kuma wannan sananne abu ne ga kowa. Bugu da kari kuma, idan ka bi tarihin wannan sabatta-juyen, zaka samu cewa matsalar ta tattaru ne bangare guda, wadanda kowanne lokaci sai dai abi abinda suke so, kuma ba zasu taba yarda wani ya shiga gaba su bi ba, sai dai a bi su, to wannan shi ne rikicin, har yau.”

Ya ce, a lokacin yake jan ragamar jam’iyyar, yayi iya kokarin sa wajen dinke barakar da ya tarar- wadda ta kunshi bangaren tsohon ministan hukumar yan-sanda, Adamu Waziri da bangaren marigayi Sanata Usman Albaishir hadi da yan-baruwan mu.

“Wanda muka yi kokari wajen gudanar da zaben sabbin shugabanin jam’iyyar wadanda suka kasance karbabbu ga kowanne bangare, a 2012. Baya ga wannan, kan ka ce me, sai uwar jam’iyya ta kasa a karkashin Adamu Mu’azu ta tsunduma cikin rikicin shugabanci. Sannan da hargitsa tamu PDP a jihar, wanda ta rusa zababbun shugabanin- haka kawai ba tare da wani dalili ba, wanda daga bisani kuma ta nada wani kwamitin rikon kwarya na jeka-na-yika, lamarin da ya jwo muka fadi zabe”.

“Tun bayan wannan ne, jam’iyyar PDP ta fada cikin rikita-rikita wanda daga bisani Sanata Ali Modu Sherrif ya kawo wa PDP dauki tare da maido ta cikin hayyacin ta. Wanda a zamanin Modu Sherrif ne zangon shugabanin jam’iyyar ya kare tare da sake zaben wasu sabbi a cikin nasara, ciki kuwa har da a nan jihar Yobe; inda kusan kammala zaben ne wasu suka janye saboda yadda sakamakon bai zo musu yadda suke so ba”. Inji shi.

“Saboda haka, tun daga wannan lokacin kawunan yan jam’iyyar ya rarrabu. Wanda shima bayan zuwan Sanata Ahmed Makarfi ya kara iza wutar rarraba kawunan yan PDP wadanda kaso 90 cikin 100 a jihar Yobe suna tare da Sanata Ali Modu Sherrif.”

“Wannan ya zo ne saboda yadda a wasu jihohin an rusa shugabanin tare da basu umurnin sake zabar sabbi, amma mu da yake yayan bora ne, bamu samu wannan tagomashin ba. Wanda hakan ya sahale wa Adamu Waziri hanyar dora sabbin shugabanin kashin kan sa”.

Yerima Ngama ya ce, a yekuwar da suka yi- mai suna ‘Karasuwa Declaration’ ya ce a ciki sun bibiyi komai filla-filla dangane da jam’iyyar, kama daga 2011 zuwa yau, wanda kuma a ciki suka cimma matsayar cewar, wanda shi ne hanya daya tallin-tal da PDP zata bi wajen samun karbuwa ga jama’ar Yobe tare da kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai jan ragamar jihar Yobe.

“Hukuncin da kotu ta aiwatar shi ne kan cewa, zababbun shugabanin jam’iyyar a karkashin Lawan Gana Karasuwa an yi shi bisa tsari kuma akan dokoki, an rantsar dasu tare da damka musu takardar shaidar zaben. Duk da wannan kuma, sai kwamitin NEC na kasa a karkashin Makarfi suka yi amfani da karfin ikon su wajen sake gudanar da wani zabe ba tare da sun rusa shugabanin da aka zaba a baya ba”.

Bugu da kari kuma, ya ce taron nasu ya cimma batsayar raba tafiyar su da bangaren Adamu Maina Waziri a siyasance, “ba mu ba Adamu Waziri a cikin kowanne irin lamari wanda ya shafi jam’iyyar PDP- ba zamu taba hada tafiya tare da su ba.”

Inda a karshe ya bayyana cewa bangaren su ya ayyana cewa suna sauraron alkiblar da Sanata Ali Modu Shariff zai fuskanta a siyasance, a matsayin inda zasu fuskanta. Wanda yar manuniya ke tabbatar da cewa suna iya ficewa su bar tsohuwar jam’iyyar tasu ta PDP.

 

Exit mobile version