Bani Da Alaka Da Fastocin Siyasa Da Ake Likawa Da Hotona –Muntari Lawal

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ya nisanta kansa da wata fosta ta siyasa da aka yi amfani da hotansa  yana neman tsayawa takarar Sanatan Katsina ta tsakiya a zaban 2023 mai zuwa.

A jiya asabar ne dai aka wayi gari an lika wadannan fostoci a manya –manyan titunan cikin garin Katsina inda nan da nan labarin ya cika gari da kuma kafar sadarwa ta social media cewa gogarmar dan siyasar yana neman tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya.

To sai dai, shima bai yi kasa a gwiwa ba, ba tare da bata lokaci ba ya kira taron manema labarai inda ya karyata wannan batu tare fa fadin cewa akwai masu san tada fitina a cikin jam’iyyar APC shi yasa suka bullo ta wannan hanya.

“Ni a tunina idan kauna ce ake nuna mani, ya kamata a tuntube ni ko a shawarceni, aji daga bakina, ba wai kawai ayi amfani da fostocina a cikin gari ba ana cewa zan tsaya ko kuma na tsaya takarar Santa a zabe mai zuwa ba.” Inji shi

Ya kuma yi nuna da cewa idan ba a manta ba wanda yake kan wannan kujera yanzu haka, surukinsa ne, sannan kuma bakwabcinsa ne, haka kuma ba wani laifi ya yi ba da za a bijiro da wannan fitina ba.

Muntari Lawal wanda shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina kuma shi ya jagoranci kwamitin Shirya Zaben Shugabannin jam’iyar APC  da ya gudana kwanan nan a jihar ta Katsina.

Ya ce ba zai taba tunanin tsayawa neman takarar ba a ko wane irin mukami ba. Ya kara da cewa har yanzu yana kan biyayya ga matsayi ko ra’ayin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, duk inda ya ce su yi nan za su yi.

Alhaji Muntari Lawal ya kara da cewa masu neman kawo rikici acikin jam’iyar APC a jihar Katsina sune ke yada irin wannan labarin wanda ya bayyana shi da cewa tamkar wani nau’I ne na cin fuska da mutunci da kuma Wulakanci.

Kazalika ya yi kira ga mutanan jihar Katsina cewa shi yana nan akan bin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari sau da kafa, kuma idan gwamnatin ta gama wa’adin ta, toh zai koma gonar shi kamar yadda maigidanshi gwamna Masari zai koma gona shima.

Exit mobile version