Rabiu Ali Indabawa" />

Bankada: Shekaru Uku Kauyenmu Yana Hannun Boko Haram, Cewar Kakakin Majalisar Borno

Duk da cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tana ikirarin babu wani gari da yake hannun kungiyar Boko Haram, amma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkareem Lawan, ya ce, shekaru uku kenan babu mutum a kauyensu na Guzamala, yana mai cewa, idan ban da ’yan ta’adda, babu kowa a karamar Hukumar.

Don haka sai Shugaban majalisar dokokin ya kuma musanya maganar cewa, Boko Haram ba su rike da wata karamar Hukuma a Jihar Borno.
Jaridar yanar gizo ta Premium Times ta rahoto Rt. Hon. Abdulkareem Lawan ya na raddi ga wasu kalamai da suka fito daga bakin tsohon babban hafsan tsaron kasa, Janar Gabriel Olonisakin a wajen yi wa tsofaffin shugabannin sojojin kasar bikin ban-kwana, inda Janar Olonisakin ya yi ikirarin babu cewa, yankin da ke hannun ‘yan ta’adda a yau.
Hon. Lawan ya ce ko kadan ba haka abin ya ke ba, inda ya ce, idan aka fadi haka, to ba a yi wa mutanen Borno, musamman na mazabarsa, adalci ba.
Lawan ya kara da cewa, duk da yana shugaban majalisar dokoki, shekaru uku kenan bai isa ya kai ziyara zuwa kauyensu ba, saboda ‘yan ta’addan ke rike da yankin.
“Ban yarda da ikirarin da tsohon hafsan tsaro ya yi wajen bikin yi masa sallama, da ya ce babu wani yanki a Nijeriya da ke karkashin Boko Haram ba.” In ji Lawan.
Jaridar ta ruwaito shi ya na cewa: “Ina cewa wannan ne domin gaba daya karamar Hukumata, tana hannun ‘Yan Boko Haram na tsawon shekaru uku da suka wuce.” “Yanzu haka da na ke maka magana, babu wani mutum guda da ke zaune a karamar Hukumata, Guzamala, abin takaici babu ko kanshin sojoji a kauye (Guzamala).”
Ya ce kafin yanzu, a wajen wani taro da aka yi a 2020, Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ya yi irin wannan ikirari, wanda sam ba gaskiya ba ne. ‘dan siyasar ya ce gwamnatin nan mai-ci ta yi kokari bayan ta hau mulki, amma a cewarsa, maganar karbe ko ina daga hannun Boko Haram, ba gaskiya ba ne.
A jiya ne mu ka ji cewa ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun yi ta’adi da ya sa aka yi kwana da kwanaki babu wutar lantarki a babban birni Maiduguri, Jihar Borno. Mutanen garin Maiduguri da kewaye su na zaune a cikin duhu bayan ‘yan ta’addar Boko Haram sun lalata wani babban layin wutar da ya jawo lantarki zuwa jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN, ya ce, abubuwa sun tsaya cak sakamakon lalata wutar lantarkin da Boko Haram suka yi.

Exit mobile version