Connect with us

KASUWANCI

Bankin Afredim Ya Zuba Jarin Dala Biliyan 17 A Nijeriya

Published

on

Bankin African Edport-Import (Afredim bank) ya amince zuba dala biliyan 17 a hada-hadar kasuwancin Nijeriya tun a lokacin da ya fara gudanar da ayyukan sa a shekarar 1994 da kuma a cikin watan Disambar da ya gabata.
Shugaban bankin Dakta Benedict Oramah ne ya sanar da hakan a lokakcin da ya jagoranci tawagar bankin don kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa.
Dakta Oramah ya ce, bankin kayan bankin ya taimaka matuka wajen habaka manyan fannonin tattalin arzikin Nijeriya kuma bankin ya bayar da bashin da ya kai kimanin dala biliyan 3.5 a Nijeriya tun daga 31 ga watan Disambar 2017.
Shugaban ya zayyana cewar, fannonin da suka amfana da bankin a Nijeriya sun hada da; cibiyoyin hada-hadar kudi da sufuri da masana’antu da bangaren kayan noma da mai da iskar gas da wutar lantarki da kuma hanyar sadarwa.
Har ila yau Dakta Oramah ya ci gaba da cewa, sauran taimakawar da bankin ya yi Nijeriya sun hada da; bayar da taimakon dala biliyan 1.8 don tallafawa tattalin arzikin Nijeriya a lokacin da kasar ta shiga matsalar farashin mai daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2016.
Shugaban ya kara da cewa, bankin ya kuma samar da tsari da samar da layiyyuka kasuwancin zuba kudi na sama da dala miliyan 800 a lokacin ci gaba da bankin wanda bankuna da dama na kasa da kasa suka yanke layuyyukan su na bayar da bashi daga kasar.
Shugaban ya sanar da cewar, a yanzu bankin ya samar da shirye-shirye a Nijeriya wadanda suka hada da; samar da gwaji na ci gaba da duba cibiyoyi dake fain kasar nan ta hanyar yin hadaka da hukumar tabbatar da ingancin kaya ta kasa(SON), don a kafa ingantacciyar cibiyar kiwon lafiya da kuma shiga kamfanin zuba jari na Nijeriya wanda gwamnatin Nijeriya ta daukaka shi don bai wa masana’antu kwarin gwaiwa ta hanyar ayyukan da suke gudanarwa da ta hanyar basu basussukan banki da kuma bayar da wasu basussukan da suka kai dala miliyan 750 ga bankin masana’antu a cikin watan Yuni.
Shugaban ya kara da cewar, bankin nasu ya kuma samar da hanyar kasuwanci da rabar da wasikun bayar da layuyyukan bashi ga dukkan bankunan dake Nijeriya, ta hanyar yarjejeniya da babban bankin kasa(CBN) don a tabbatar da sukunin samun kadi gudanar da kasuwanci da
kuma ci gaban cibiyar bankin Afredimbank ta kasuwanci dake Abuja.
Dakta Oramah ya kara da cewa, Bankin a shirye yake don yin aiki da gwamnatin tarayya yadda zai zuba kudi da suka kai dala biliyan daya don tallafawa zuba jarin gwamnatin akan kasuwanci.
Ya gayyaci shugaba Buhari da kuma gwamnatin tarayya zuwa taron bankin na shekara da za a gudanar daga ranar 11 zuwa 14 ga watan Yuli a Abuja.
Dakta Oramah ya kuma sanarwa da shugaba Buhari cewar bankin zai gudanar baje kolin cinikayya na nahihar Afrika daga ranar 11 zuwa 17 na watan Disamba don daukaka cinikayya a kasashen Afrika.
Da yake mayar da jawabi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya godewa Dakta Oramah akan ziyarar da ya kawo ya kuma yabawa bankin akan taimakawar da ya yi akan tattalin arzikin kasar nan da kuma habaka kasuwanci a nahiyar Afrika.
Buhari ya kuma yi kira ga mahukuntan bankin dasu kara taimakawa fannin noma na kasar, musamman don inganta samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: