Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Bankin Bunkasa Noma da Ruwa, ya Sanarwa al’ummar kasar nan Dala biliyan dari hudu domin bunkasa noma da ruwa da ma’adanai, Daraktan Bankin Abdirrazaw Oyinloye ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci mukaddashin gwamnan Zamfara Malam Ibrahim Wakala, a gidan gwamnati.
Daraktan ya bayyana cewa” Wannan shiri ne da gwamnatin tarayya ta samar da shi a karkashin ma’aikatar ruwa, kuma zata ba da kashi goma daga cikin dari, sai gwamnatin jihohi kuma su bada kashi biyar,shi kuma Bankin zai ba da kashi tamanin da biyar. Don inganta noma da albarkatun ruwan da ma’adanai a fadin wannan Kasar nan.
Anasa jawabin mukaddashin gwamna Malam Ibrahim Wakala ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Zamfara, na kokarin inganta madatsar ruwa ta Gusau.kuma tuni aka ba kamfanin, Cana Construction company watau (CGC) kwangilar samar da ingantacen ruwa a Gusau da kuma fadin Jihar baki daya.