Daga Yusuf Shuaibu
Babban Bankin NIjeriya (CBN), na ci gaba da karbar takardun neman rancen Naira Biliyan 50 da aka yi niyyar bada wa (TCF) da nufin tallafawa magidanta da masu kananan da matsakaitan masana’antu (MSME), wadanda annobar COBID-19 ta shafa.
Tallafawar wanda bankin koli ya kafa a watan Maris na shekarar 2020, ana bayar dashi ne ta hanyar Bankin bada rance na asali mai karfin hadin gwiwa (NIRSAL).
Yayin da yake sanar da bude kofar a wani sako a ranar Litinin, bankin ‘NIRSAL Microfinance (NMFB)’ ya ce, masu neman takardun dole ne su kasance magidanta da ‘yan kasuwa, tare da tabbatattun shaidun tabbatar da rayuwar su wanda cutar korona ta shafa.
Kamfanoni da ke da shirin banki don amfani da damar da ta samo asali daga cutar COBID-19 suma sun cancanci nema.
Kudin ribae zai kasance kashi tara a kowace shekara, babban aikin zai kasance na tsawan shekara guda, ba tare da zabin sakewa ba.
An saita babban kudin aiki da za a mika wa ‘yan kasuwa masu cancanta akalla da kashi 25 cikin dari na matsakaicin sauyin shekara uku da suka gabata.
Haka zalika, idan kamfanin bai kai shekaru uku yana aiki ba, za a bayar da kashi 25 cikin 100 na shekarar da ta gabata.
Lamunin lokaci yana da iyakar abin da ba zai wuce shekaru 3 ba tare da akalla dakatar da shekara guda ba.
Magidanta za su iya samun damar mafi girman rance na Naira miliyan 3, yayin da za a kayyade adadin rancen ga SME din gwargwadon kudi da girman masana’antar masu cin gajiyar, wanda ya dogara da akalla Naira miliyan 25.