Abubakar Abba" />

Bankin Diamond Ya Yi Wa Kananan ’Yan Kasuwa Kyautar Naira Miliyan 15

A bisa kokarin inganta tsakaitan kasuwanci, Bankin Diamond Plc ya baiwa ‘yan kasuwa biyar da suka ci nasara a  karkashin shirin sa na karo na shirin na bakwai ha habaka kasuwanci naira milyan sha biyar.

Babban Daraktan Banki Uzoma Dozie, ya bayyana cewar, wadanda suka yi nsarar su biyar, ko wannen su an bashi naira milyan uku bayan da sukashafe watanni shida ana basu horo a jami’ar Pan Atlantic Unibersity dake cikin jahar Legas.

Mista  Dozie yaci gaba da cewa,Bankin ya yi hadaka ne da sashen kasuwanci na jami’arta Pan Atlantic, inda ya yi nuni da cewar sama da matsakaitun sana’oi dari uku da hamsin ne suka amfana da shirin tun lokacin da aka Bankin ya kirkiro da shirin a shekarar 2011.

A cewra Mista Dozie, manufar shirin shine a baiwa masu matsakaitun sana’oi kwarin gwaiwa don habaka kasuwancin su, inda ya kara da cewar shirn ana son ya wuce tsyawa a cikin aji kawai.

Shima a nashi jawabin Daraktan EDC Mista Peter Bankole yace, cibyar  ta yi hadaka da banki ne a shekaru bakwai da suka shige.

Mista Bankole ya kara da cewar cibiyar itace ta bayar da shawarar kirkiro da shirin da kuma tabbatar da an wanzar dashi har da zakulo wadanda suka shiga shirn aka fafa ta dasu, inda wasu suka samu nasara.

A cewar  Mista Bankole, Bankin ya kara zurfafawajen horas da yan kasuwar akan yadda zasu tafiyar da kasuwancin su da kuma yadda zasu samu damar samun bashi harda basu shawarwari.

Ya kara da cewar, habaka sana’oi kanan har guda hamsin, a duk shekara zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasa.

Itama a nata jawabin shugabar sashen yada labarai na Bankin Mista Chioma Afe yace, Bankin ya bayar da naira  miliyan 105 kyauta ga mutane biyar da suka ci nasara a karkashin shirin a cikin shekaru bakwai da suka wuce.

Afe tace baya ga kkyautar, hakan kuma zai taimak wajen rage rashin aikin yi a kasar nan da kuma karfafa kasuwanci da zasu yanyo samar da ayyukan yi.

Ta yi nuni da cewar daliban a karkashin shirin baya ga ilimin da suka samu a karkashi EDC, daliban zasu kuma samu sukunin samun bashi daga kungiyoyin kasashen duniya kamar daga Bankin Mta na Duniya.

A cewar Afe  za kuma a basu horo na musamman yadda zasu gudanar da kasuwancin, kuma a karshen tantance mutane hamsin zasu yi watanni shida ana horar dasu a karkashin shirin a jami’ar ta Pan Atlantic.

Ta bayyana cewar, za’a a zabo wadanda suka yi ficen su sha biyar za’a basu horo a zagayen shirin na biyu, inda za a bukace su dasu gabatar da dabarun kasuwanci na zamani.

Ta ce, a karshen shirin wadanda suka shiga cikin gasar mutane biyar da suka gabaar da tsarin kasuwanci da yafi ko wanne, Bankin zai baiwa ko wanne su naira miliyan uku don habaka kasuwancin su.

Wadanda suka ci nasarar su bakwai sune, Ikenna Ubah da Tope Alake da Jumoke Dada da Bayo Ojelabi da kuma Osagie Azeta.

Exit mobile version