Bankin Duniya da hukumar bayar da lamuni ta duniya (IMF) sun amince da bai wa Nijeriya bashin dala biliyan 11.465 a wannan shekara.
A cikin watan Afrilu, IMF ta bai wa gwamnatin tarayya kudade na dala biliyan 3.4 a matsayin tallafi ga Nijeriya domin dakile cutar Korona.
A cikin watan Mayu, Bankin Duniya ya bai wa Nijeriya karin dala miliyan 176 a matsayin tallafin kudade na farfado da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gas. An bayar da wadannan kudaden ne domin tallafa wa mutanen yankin. Domin bunkasa a kan cutar Korona, a ranar 7 ga watan Agusta, Bankin Duniya ta amince da bai wa Nijeriya dala miliyan 114.28 domin tallafin cutar Korona.
Nijeriya ta amso basuka da dama wadanda suka hada da dala miliyan 100 daga kungiyar bunkasa kasa da kasa da kuma tallafin dala miliyan 14.28 daga kudaden taimakon gaggawa a kan cutar Korona. Tun da farkon wannan shekarar dai, Bankin Duniya ya ci gaba da taimakawa kasashe a kan cutar Korona, wanda ya taimaka wa Nijeriya da dala miliyan 200 donmin farfado da kananan kasuwanci.
Bugu da kari, ta kai kayayyakin Nijeriya wanda kudadansu ya kai na dala 8.4 a wannan shekarar, a ranar Talata ce, Bankin Duniya ya amince da bai wa kasan dala biliyan uku. A kalamun Bankin Duniyan na jiya, ya ce ya amince da gudanar da ayyuka guda biyu a Nijeriya wadanda kudadansu ya kai na dala biliyan 1.5.
“Wadannan ayyuka za su taimaka wajen kara inganta mahimman ayyuka da bayar da tallafi ga talakawa da magidanta wadanda suke bukata. Haka kuma zai karfafa samar da abuinci ga magindanta wadandea suke bukata da farfado ka kananan harkokin kasuwanci. Duk wadannan yana daga harkokin kudade,” in ji Bankin Dunuya.
A aiki na biyu kuma wanda yake karkashin kungiyar kasa da kasa zai lakume dala miliyan 750 wajen samar da ayyukan dai-daita sha’anin kudade. Ayyukan zai kawo ci gaba a dukkan jihohi 36 tare da bayar da tallafi a kan cutar Korona.
“Sauran kudaden za a yi amfani da suka waken shirin nan na cike tazarar kudade saakamakon raguwar samun kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke mafa da shi a halin yanzu.
“Haka kuma zai taimaka wajen kara ci gaba da kashe kudade ta hanyar da ta dace da kara karfafa haraji wanda zai sa gwamnati kammala ayyukan da ta sa a gaba a dukkan jihohin kasar nan.”