Connect with us

LABARAI

Bankin Duniya Ta Samar Da Dala Miliyan 60 Don Ayyuka A jihar Ogun

Published

on

Bankin duniya ta samar da dala miliyan 60 domin ayyuka a Jihar Ogun. Bankin ya amince ya bayar da wannan taimakon ne domin bunkasa ayyukan gona a yankunar karkara cikin Jihar, wanda ya gudana tare da hadin gwaiwar gwamnatin Jihar domin samar da kudadan.

Jami’in gudanar da ayyukan Samuel Onabanjo shi ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, a wani bangaran shirin bankin duniyan wajen bayar da tallafi a kan ayyukan yi, ya kara da cewa gwamnatin Jihar Ogun ta saka naira miliyan 713 a cikin kudadan domin aiwatar da ayyukan. Onabanjo ya bayyana cewa ita ma gwamnatin tarayya ta ba da na ta tallafin kudin aikin, ba a gudanar da komi ba cikin shekaru uku na aikin amma sakamakon irin kokarin da muka yi domin a aiwatar da aikin, ya sa mun yi aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki a kan lamarin.”

Ya ci gaba da cewa “bankin duniya da wadansu hukumomi masu bayar da tallafi, sun bayar da dala miliyan 60 domin ayyukan a Jihar Ogun.

“Gwamnan Jihar Ibikunle Amosun ya bayar da naira miliyan 344 a shekaran da ta gabata, yayin da ya bayar da naira miliyan 369 cikin wannan shekaran na 2018, ga  wannan ayyukan wanda za a gudanar a cikin Jihar.

“Gwamnatin Jihar za ta dauki ma’aikata tare da samar da ofisoshin ma’aikatan wadanda za su gudanar da wannan aikin.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: