Bankin Duniya Ya Yaba Wa Gwamnatin Jigawa Kan Samar Da Tituna

Bankin Duniya ya bayyana gwamnatin jihar Jigawa a matsayin ta sahun gaba a jihohin Nijeriya wajen samar da ingantattun tituna a yankunanta.

Mukaddashin gwamnan jihar ta Jigawa Barista Ibrahim Hassan Hadeja ne ya bayyana haka a yayin tattaunawarsa da manema labarai a birnin jihar dake Dutse.

Barrista Hadeja ya ce, wannan mataki da jihar ta dare, ya biyo bayan irin yunkurin da gwamnati me ci a yanzu a jihar ke yi na gudanar da ayyukan raya kasa domin bunkasar jihar da al’ummarta baki daya.

Haka kuma ya bayyana cewa, harwayau a sakamakon da Bankin duniya yafitar, jihar ta Jigawa ta kuma samin zama mataki na biyu cikin jihohi 36 dake fadin wannan kasa a wajen gudanar da mulkin adalci ba tareda nuna wariya ga wani yanki ba.

Sannan ya kara da cewa, Bankin Duniyar ya kuma bayyana Jihar ta Jigawa a matsayin ta hudu  wajen samarda ingantaccen ruwansha da kuma kayayyakin more rayuwa.

Mukaddashin gwamnan ya kuma bayyana kudurin gwamnatin jihar na bunkasa rayuwar al’ummar jihar a wannan shekara ta 2018 da muka shiga.

Daga karshe ya yi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da marawa yunkurin gwamnatin baya karkashin jagoran gwamna Muhammad Abubakar Badaru domin cigaba da samarda ayyukan raya kasa baki daya.

Exit mobile version