Bankin FMBN Ba Zai Wadatar Da Al’umma Da Gidaje Ba –Adamu

Daga  Sabo Ahmad

Shugaban kungiyar masu gina rukunin gidajen sayarwa (AHCN). Muhammad baba Adamu, ya bayyana cewa, duk da kokarin da Bankin bayar da bashin gina gidaje ke yi na ganin ya samar da gidaje ga dimbin al’umma bai hana kullum bukatar gidajen ta na kara karu wa ba.

Adamun yafadi hakan ne a lokacin da kungiyar tasu ta kai ziyara hedikwara Bankin da ke Abuja, inda ya yaba wa Bankin bisa kokarin da yake na samar da gidaje ga al’ummar kasa.

Shugaban ya ci gaba da cewa, “muna sae da irin matsalolin da ake ciki na mallakar gidaje a wannan kara da kuma kokarin da gwamnati ke yin a fuskantar wannan babban kalubale da ke gabanta”

Sai ya kara da cewa, kokarin da kungiyar tasu ta dade tana yi shi ya haifar da samar da, Hukumar gina gidaje ta kasa da Cibiyar binciken ingancin gini da hanyoyi ta Nijerya da wadansu tsare-tsaren gina gidaje na shekara ta 1999 da Asusun tallafin gina gidaje na kasa da kuma Bankin bayar da rancen gina gidaje.

Dangane da batun tsadar kayayyakin gini kuwa, shugaban ya ce, “muna kokarin hadin gwiwa da bankin FMBN da Cibiyar Bincike ta NBRRI na inganta kayan ginin da muke da su a wannan kasa, don a samu saukin mallakar gidaje”. Ya ci gaba da cewa, duk da kalubalen da ake fuskanat, a halin yanzu masana na ta kokarin ganin sun samo bakin zaren warware wannan matsala na karancin gidaje a dukkan fadin kasar nan.

Shugaban ya kara da cewa, an kulla irin wannan yarjejeniyar hadin gwiwa lokacin tson shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda Cibiyar binciken ingancin gini da hanyoyi ta Nijeriya inga Hukmar gidaje ta jihar Ekiti ta gina gida 225.

Shuban ya ci gaba da bayanin cewa, Bankin FMBN da Cibiyar Bincike ta NBRRI suka samar da kudi da tsarin gina gidajen, kungiyar tasu kuma ta AHCN ta samar da filin ginin da hadin gwiwar Asusun talafin gini na kasa, wadanda suka gina rukunin gidaje a jihar Kaduna da Kwara da Abiya.

Ya bayyana tashin farashin kayan gine-gine a matsayin babbar barazanar da ta haifar da matsalar karacin gidaje, wanda kuma shi ne musabbain karaci gidaje

Adamu ya kara da cewa, shirye-shirye sun yi nisatsakaninsu da Babban Bankin Nijeriya na samar da kudi naira biliyan 500 don gina gidaje a dukkan fadin kasar nan, wanda za a yi batare da hadin gwiwar FMBN ba.

Exit mobile version