Connect with us

KASUWANCI

Bankin Heritage Ya Samu Yabo Kan Bunkasa Harkar Gona

Published

on

Bankin Heritage Plc ya zamo zakara, inda aka bashi lambar yabo  a fannin matsakaitan sana’oi da kuma karin samun wata lambar yabon akan kokarinsa na bunkasa harkar gona ta 2018. A cikin sanarwar da Bankin ya fitar, Bankin ya kuma samu lambar yabo ta shekara daga  cibiyar  CIBN ta 2018. Bankin ya samu lambar ce saboda zagewarsa wajen hado kan yayan kungiyar, shiga a dama dashi da kuma daukar nauyin shirye-shiryen cibiyar. Har ila yau, Bankin ya samu lambobin yabon ne saboda yadda yake gudanar da salon shugabanci, samar da ci gaba, habaka fannin aikin noma da kuma matsakaitan sana’oi.

Acewar sanarwar da Bankin ya fitar, Muallar CFI sananniya ce wajen wallafa labarn kasuwznci, harkar hada-hadar kudi kuma shalkwatar ta, tana kasar Ingila ne.Ta kara da cewar, Sanarwar taci gaba da cewar an bawa Bankin lambar yabon ne bayan amiccewar da CFI ta yi ta hanyar yin zabe tare da hadin gwaiwar abokan hudda na Bankin Duniya, Hukumar Bayar da Lamuni ta duniya IMF,  Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Majalisar Dinnin Duniya UN da kuma  IFC. Taron wanda ake gudanar da shi duk shekara kamfafin aikin noma na, AgroNigeria ne ya shirya shi da nufin zakulo maza da mata, fannin kasuwanci,da kuma cibiyohi da suka bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen habaka aikin noma.

Da yake jawabi akan lambobi, sabon,Manajin Darakta kuma Babban jami’I na Bankin Heritage Ifie Sekibo, an ruwaito yana cewa,” lallai an karrama mu a bisa bamu wannan lambobin yabon da wadannan cibiyoyin suka bamu da suke lura da fannin noma da matsakaitan sana’oi wadanda manya ne a fannin habaka tattalin arzikin kasa kuma wannan yana nuna yadda Bankin ya samu nasarori wajen uya gudanar da ayyukan sa.” Acewar sa, Bankin Heritage shine akan gaba wzjen habaka fannin noma da bayar da kudi wajen habaka matsakaitan sana’oi kuma zaici gaba da bayar da gudunmawarsa ga Babban Bankin kasa CBN wajen salar da kudi ga muatene da kuma kungiyoyi akan irin kokarin da suke yi wajen na ciyar da fannonin gaba. A karshe ya ce, Bankin kuma zaici gaba da bayar da gudunmawarsa wajen habaka amfanin gina yadda manoman za su iya samun kuwin musaya na kasashen waje.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: