Bankin NEXIM Zai Raba Bashin Dala Biliyan Daya Ga ‘Yan Kasuwa

Bankin NEXIM ya sanar da cewa, ya shiga yarjejeniyar kasuwanci ta dala biliyan daya da bankin kasuwanci na Afrika AEIBN da kuma sauran kasashen waje. Rattaba hannun yarjejeniyar tana daya daga cikin kaddamar da baje kolin da aka yi a ta nahiyar Afirka a Kairo dake cikin kasar Masar. A cikin sanarwar da bankin na NEXIM ya fitar a ranara Litinin data wuce ya sanar da cewa, rattaba hannun yarjejeniyar, za’a wanzar da ita a karkashin hada-hadar kasuwancin Nijeriya da Afrika da kuma shirin zuba jari don baiwa zuba jarin goyon baya a tsskanin Nijeriya da kasashen dake cikin nahiyar Afirka. Acewar sa, a bisa yar yarjejeniyar, AFREDIM zai samar da dala biliyan daya a matsayin bashi, wadda bankin NEXIM ne zai samar da ita don a tsallake siradin hayewa na amfana da ayyukan da kuma hada-hadar kasuwsnci da zuba jari. Acewar yarjejeniyar, an samar da kudin a wadace don habaka hada-hadar kasuwsnci tsakanin Nijeriya da sauran kasashen dake cikin nahiyar Afirka. Sanarwar ta bayyana cewa, dala biliyan dayar zata taimaka wajen samar da kudin shiga da kuma ayyukam yi ga yan kasar nan. Har ila yau, an samar dasu a wadace don bayar da tallafi ga hada-hadar kasuwanci da kuma zuba jari. A jawabin sa a lokacin rattaba hannun yarjejeniyar, Manajin Darakta kuma babban jami’I na bankin na NEXIM, Abba Bello ya sanar da cewa, yarjejeniyar zata taimaka sosai wajen habaka fitar da kaya kasashen waje da zuba jari harda matsakaitan sana’oi. A karshe Abba Bello ya ce, ta hanyar yarjejeniyar bankin zai samu damar daukaka huddar kasuwanci a nahiyar Afirka kuma don a cimma wannan nasarar, bankin na NEXIM zai yi aiki da masu ruwa da tsaki harda masu safarar kaya zuwa kasashen waje, masu zuba jari, sauran cibiyoyin kasuwanci na cikin gida dana waje don cimma manufofin shirin hukumar NATIPP.

Exit mobile version