Connect with us

KASUWANCI

Bankin UBA Ya Samu Yabo Kan Kirkirar Sabon Salon Gudanar Da  Ayyuka

Published

on

Bankin UBA Plc ya zamo garzon shekara, inda aka bashi lambar yabo saboda kirkiro da sabon salon gudanar da ayyukan Banki ta zamni.  Wta Mujjalr hada-hadar kudi ta kasa da kasa ce ta shiriya taron na karrama Bankin.

A cikin wata sanarwa da Bankin ya fitar, ya bayyana cewar, ganin cewar Bankin ya tserewa sauran tsaransa, zai kara yin kaili wajen a fannin gudanar da shugabanci da kuma fito da wasu sababbin kirkire-kirkire musamman don kara habaka kasuwzncinsa. Matakan da aka dauka na bayar da lambar yabon, anyi alfani da nuna hazaka, kwarewa wajen gudanar da shugabanci, yin amfani da kafar yanar gizo da kuma yadda Bankin ya yi fice wajen yin hudda ta kasa da kasa.

Bayan anbi a sannu wajen zabo wadanda suka cancanci karbar lambar yabon, da rawagar kwararru suka gudanar bayan sunyi iya bincikensu,anhi alfani da irin nasarar da aka samu a baya.

A cewar Bankin, lambar yabon an same tane saboda iya iya gudanar da aikin Banki a bisa bin ka’ida da kuma irin dimbin nasaraorin da Bankin ya salar a baya, musamman a fannin gudanar da aikin Banki.

Da yake jawabinsa a bisa samun nasarar, Shugaban sashen yanar gizo na Bankin Austine Abolusoro ya ce, “ muna murna da kuma nuna tunkahon mu da aka zakulo lu a matsayin wadanda suka lashe gasar ta 2018.” Ya yi nuni da cewar, hakan ya nuna kokarin mu da muaka yi a baya wajen zuba jari a fannin fasaha, musamman ganin cewar ayyukan mu gudanar da aikin Banki ta hanyar yin amfani da kimiyya ya bazu har a nahiyar Afirka.

Ya kara da cewar, manufar ta tamu baza ta tsaya anan ba domin zamuci gaba da kara yin himma wajen gudanar da aikin Banki ta yin amfani da fasaha yadda zamu malaye nahiyar Afirka.

Ya kara da cewar, burinmu shine luga yadda zalu kara habaka kwarewar mu ta hanyoyi da dama.

A karshe ya ce, a bisa wannnan jarramawar da muka samu da kuma sauran kambobin yabo da luka salu a baya,muna bawa abokan huddar mu tabbacin cewar zamu kara zage damtse wajen karfafa hudda dasu da kuma ciyar da aikin Banki a gaba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: