Bankin Zenith Ya Samu Ribar Naira Biliyan 174

Bankin Zenith ya samiu riba kafin haraji ta Naira bilyan 174 a shekarar 2017, wannan kuma shi ne ya kasance kashi 24 cikin 100, wannan kuma ya nuna ke nan an samu karin Naira bilyan 140, da aka samu shekarar 2016, duk kuwa da yake an samu karuwar masu ajiye kudi da kashi 8 cikin 100, daga Naira Tiriliyan 2.55 a shekarar 2016, zuwa  Tiriliyon 2.74 a shekarar 2017.

Kudaden masu hannun jarin Bankin ya karu da kashi 15 cikin 100 daga Naira Bilyan 616 a shekarar 2016, zuwa Naira bilyan 708, a wannan shekarar da ake ciki, ya yin da kuma an samu karuwar kudaden da suke shigowa da kashi 48 cikin 100 daga Naira bilyan 455, a shekarar 2016 zuwa Naiara bilyan 674 a shekarar 2017.

Da yake jawabi a taron shekara- shekara na 27 jiya a Abuja, shugaban Bankin Mr Jim Obia ya ce, duk da yake an fuskanci wasu matsaloli, sabnoda lain da ake ciki, akwai ci gaba wanda kowa zai murna da shi.

Obia ya nuna jin dadin sa akan yadda shi Bankin ya samu ci gaba, wannan kuwa ya kasace haka ne saboda, ayyuka Bankin.

‘’Ya kara bayyana cewar ko shakka babu shekarar 2017 Bankin ya fuskanci matsaloli, saboda daga cikin gida ne da kuma waje. Amma kuma duk da hakan maganar gaskiya shi Bankin Zenith, ya yi amfanine da duk wata dama daya samu shi yasa aka samu ribar mai yawa’’.

‘’Wannan shi yasa aka samu ci gaba wanda ya gamsar da kowa, wannan kuwa kowa yana iya tunawa, da irin taka tsan tsan da muke yi da kudaden jama’a’’.

Shi ma a nashi jawabin babban jami’i na Bankin Me Peter Amangbo ya bayyana cewar shugabannin Hukumomin Bankunan sun bada tasu gudunmawar, wadda ita ma ce ta sa, aka samu ci gaban, ya kuma kara jaddada cewar. Shi Bankin zai ci gaba da yin ayyukan shi kamar yadda aka saba, zai ma, a  iya zarce nasarar da aka samu shekarar da ta gabata.

Ya dan bada wasu has ashen da ake yi a wannan shekarar kudi ta 2018 , Amangbo ya bayyaana c ewar shekarar da ta wuce an hadu da wasu matsaloli, saboda yadda aka yi ta gogayya tsakanin Bankuna, hakan kuma shi yasa muka iya tsayawa da kafafunmu, wannan ma akwai alamun da suke nuna  cewar za a dan ja daga, amma muna ba masu hulda da mu tabbacin cewar ba zamu sa su ji kunya ba.

Idan aka yi la’akari da yadda shi Bankin ya aikatu a shekarar da ta gabata, masu hannun jari sun amince akam shawarar da shugabannin Bankin suka bada, cewar a biya Naira 2.45 a ko wane hannun jari, a shekarar da ta gabata, amincewar su shugabannin Banki, wannan shin yasa a ko wanne hannun jari na Bamkin za a biya Naiara 2. 70k, wannan kuma ya biyo bayan wasu karin 25 kobo, ko wanne hannun jari,  a shekarar 2017.

Yawancin masu hannun jarin da suka yi magana lokacin da aka yi taron, sun nuna jin dadinsu akan yadda shi Bankin, saboda cika alkawarin da suka yi, akan karin ribar da suka samu, sun ce  duk da yake shi Bankin ya fuskanci matsaloli, na yadda Bankuna suka tsinci kansu, amma duk da hakan Bankin ya ci riba, ga kuma kaddarorin daya mallaka, a shekarar da ta gabata.

Exit mobile version