Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed ya bayyana cewa, bankuna na cire wadansu kudi daga cikin kason da gwamnatin tarayya ke ba kananan hukumomi a jihar domin biyan bashin da suka ci a shekara ta 2015.Gwamnan ya kuma ce, har yanzu gwamnatin jihar ba ta samu kasonta ba na Naira biliyan daya da miliyan dari shida, wandagwamnatin tarayya ta amince a bayar don taimaka wa jihohi goma sha shidan da ambaliyar ruwa ya shafa.
Kwamishinan kudi na jihar Kwara Alh.Demola Banu ne ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Ilori, babban birnin jihar Kwara.Banu ya ci gaba da cewa, kuddaden da bankunan ke cirewa daga kason kananan hukumomin biyan bashin kudin da suka karba ne, watau, Naira bilyan hudu da miliyan dari takwas a shekara ta 2015 don biyan ma’aikatansu kudin ariyas da na fansho.Dagan an sai ya yi karin haske kan kudin da aka ce mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya amince a bayar don taimaka wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa cewa, za a ba Hukumar bayar da agajin gaggawa ne, domin raba wa kai-tsaye ga wadanda abin ya shafa, ba gwamnatin jiha ba.