Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Bankuna Sun Gargadi Abokan Kasuwanci Bisa karuwar Masu Damfara A Yanar Gizo

Published

on

A na samun karuwar masu damfara a yanar gizo tun lokaci da abokana huldar bakuna suka fara amfani da wutar lantarki wajen hada-hadar kudade, tun lokacin da kasar nan aka kafa dokar hana zirga-zirga sakamakon cutar Korona. Bankuna sun gargadi abokan huldarsu da su dunga kulawa da irin hada-hadan kudade da suke yi a na’urorin wutar lantarki, domin ana karin samun karuwar masu damfara a yanar gizo.

Bankin First Bank ya samu sama da lamura na damfara wanda ya kai guda 275,000, tun daga lokacin da aka saka dokar hana zirga-zirga har izuwa rana ta yau.
Ya ce, “muna kara samun karuwar lamuran damfara a yanar gizo, wanda masu damfara suke ta kashe kudaden daga cikin asusun abokan huldarmu.
“Da farko dai, suna fara tura musa sako ne a kan katin cire kudinsu, wanda suke ce musu sun sami matsala sakamakon banbancin da aka samu a cikin takardar haihuwarsu. Inda za su bukaci su tura musu lambobin da ke cikin katin cire kudinsu, domin su damfare su.
“Da zarar sun tura musu sai su yi amfani da wadannan lambobi na jikin katin cire kudi su kwashe duk wani kudi daga cikin wannan asusu.
“Domin haka ne muke kira ga duk wani abobikin huldarmu da ya kuda da irin wannan sako, da zarar ya samu wannan sako, to ya yi gaggawar goge shi daga cikin wayarsa.
“Bankin First Bank ba zai taba taimayar ka bayananka ba ta hanyar wata lamba na daban. Ko kuma ya taimayeka na yanar zigo a kan bayanan asusun bankinka kamar irin su lambar BbN ko cikakken bayani a kan katin cire kudinka ko PIN dnka ko kuma lambar OTP.”
Haka shi ma bankin Access Bank Plc ya gargadi abokan huldarsa a kan su dunga kulawa da masu damfara ta yanar gizo, domin ayyukansu yana ta kara karuwa a cikin kwanakin nan.
Ya ce, “tun lokacin da cutar Korona ta barke a Nijeria ake samun karuwar masu sace wa mutane kudade daga cikin asusun bankinsu ba tare da sun sani ba.
“Wannan lamari yana kara karuwa musammam ma lokacin da suke nuna wa mutane cewa, su wakilan bankuna ne, inda suke samun bayanan asusun bankin abokan huldaarmu kamar irin su lambar BbN da kuma sauran mahimman bayanai.”
Shugaban bankin Access Bank Plc, bictor Etuokwu, ya bayyana cewa, bankin Access Bank baya tura wa abokan huldarsa wani sako ta waya tare da tambayar su cikakken bayani a kan bayanan abubun bankinsu.
“Ya kamata abokan huldarmu su sani banki ba zai taba tambayar lambar BbN ko PIN lambar katin cire kudi ga duk wani abokin huldar wannan banki. Bankin Access Bank ba zai taba tura wa abokin huldar bankin a kan sakon waya ko na email a kan cikakken bayani ga asusun bankinsu, dukkan irin wannan damfara ce, domin haka ya kamata mutane su dunga kulawa da irin wadannan masu damfarar,” in ji shi.
Da ya ke gargadin abokan huldarsu, bankin Fidelity Bank ya bayyana cewa, ya kamata abokan hulda da su kula da masu damfara a yanar gizo wadanda suke amfani da lokacin cutar Korona suna damfarar mutane kudade masu yawa daga cikin asusun bankinsu. Bankin ya bayyana wasu daga cikin hanyoyin da wadannan masu damfara suke amfani da su kamar haka, kar mutum ya danna duk wani sako da ya shigo cikin wayarsa ana tambayarsa cikakken bayani a kan asusun bankinsa, a goge irin wannan sako da zarar ya shiga cikin waya. Idan ka ga an kara tura maka a wayarka, to ka yi kokarin tuntubar wakilin bankika cikin sauri.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: