Abdulrazaq Yahuza Jere,
Da farko kafin in bayyana bankwanata da Shugaba Sam Nda-Isaiah, zan yi waiwaye a kan wani alherinsa gare ni. A lokacin da na wallafa katin gayyatar daurin aurena da aka yi a Satumbar 2018. Na rubuta sunansa a katin da zan gayyace shi, sai na dauka na nufi ofishin Manajan Daraktan Kamfani a wancan lokacin, Malam Abdul Gombe da nufin ko zai taimake ni ya bai wa Shugaba Sam hannu da hannu. Bayan na ba shi nasa, sai na tambaye shi ko Shugaba Sam yana kasa bai yi tafiya zuwa waje ba, Malam Abdul Gombe ya ce mun “yana nan, kuma kar ka bari ya ji labarin aurenka a wurin wani, ka je da kanka ka gayyace shi”.
Take na karbi shawarar na fito. Caraf sai na hadu da Malam Murtala Kano da yake aiki a sashenmu na dab’i, na ce masa ina son zuwa gidan Ciyaman, ya ce ai kuwa ya ba su lokaci za su gana da shi da karfe 6 na yamma. Na ce masa don Allah idan za su je zan bi su, ya ce mun za su je ne tare da Janar Manaja na Ofishin Ciyaman, amma babu damuwa zan iya bin su.
Da muka isa gidan Shugaba Sam, sai su Murtala suka ce ni in fara shiga. Na shiga falonsa na same shi zaune tare da wasu mutum biyu a kujerar da ke damansa. Yana waigowa don ya ga wane ne ya shigo, sai ya gan ni a tsaye. Ya ce mun “na ba ka lokacin ganawa ne ka zo?” na ce masa a’a, sai na fitar da katin gayyatar. Yana gani sai ya ce mun “za ka yi aure ne?” na ce eh; Yallabai, sai ya mika hannu da ya karbi katin. Bayan ya duba, sai ya ce mun, “bari mu gani to”, daga nan ya dubi mutum biyun da suke tare da shi ya ce musu “wannan yana daya daga cikin Editocinmu na Hausa, kuma suna yin aiki mai kyau”, mutanen suka jinjina mana, na yi sallama da shi na fito.
Zuwa can anjima sai na ga an aiko mani da Naira Dubu Dari. Na binciki wasu da nake zaton ko su ne suka aiko? Suka ce ba su ba ne, nan take kawai na ce sakon Shugaba Sam ne. Na aika masa da sakon godiya kuma ya ba ni amsa. A takaice, baya ga iyayena, Shugaba Sam shi ne ya ba ni gudunmawar kudi mafi tsoka a bikin aurena. Allah ya saka masa da alheri.
Tabbas zan ci gaba da tunawa da shi da alheransa duk da cewa yana da ajizancinsa.
Tun da na kama aiki a LEADERSHIP shekara takwas cif-cif, sau daya tak na taba ganawa ni da shi ba tare da kowa ba. Abin kuwa ya faru ne du-du-du bai fi saura wata daya ya rasu ba. Na gama aikin tsara bangon farko na kira shi, ga mamakina sai ya daga, saboda ya saba ba ya dagawa, yakan bar wayar ta gama kadawa, domin ya san batu ne na duba bangon farko kawai. Yana dagawa ya ce mun “Abdulrazak, ina son ganin ka.
Ka zo gobe (Juma’a) ka same ni a gidana da karfe 8 na dare”, na ce to Yallabai. Na isa gidansa sai ga wani shi ma ya zo wurinsa, duka muka jira shi a falo. Zuwa can anjima ya shigo, bayan mun gaisa sai ya ce mun, “Abdulrazak, ka san wannan (ya nuna mutumin da ya zo ya same ni?” na ce “a’a”, ya fada mun sunansa (na manta gaskiya), ya ce “shi ne tsohon Editan Daily Trust. Ya aka yi kana Edita amma ba ka san abokin aikinka ba”, na ce ai Yallabai mun fi sanin juna idan muna haduwa a wurin taruka ko wasu hidindimu.
Sai ya nuna mun dayan falonsa ya ce in shiga ciki in jira shi. Zuwa anjima kadan ya shigo, ya ce mun “an fada mun kokarin da kake yi ta fuskar kasuwanci a A Yau. Zan nada ka Daraktar Kasuwanci na bangaren labaru, za ka iya?”, na dan yi shiru ina tunanin yadda lamarin aiki da Shugaba Sam yake musamman ta fuskar abin da ya shafi nemo kudi; na numfasa! Na ce masa Yallabai; ba zan iya ba. Ya ce “to shikenan”. Sai ya ce mun “ko kana da wata magana?” Na ce masa eh. Na yi masa bayani dalla-dalla a kan yadda na kulla alakar kasuwanci tsakanin LEADERSHIP A Yau da Sashen Hausa na Radiyon Kasar Sin (CRI). Ya nuna jin dadinsa, daga nan ya kara karfafa mun gwiwa ya ce in ci gaba da yin hakan. Muka yi bankwana na tafi.
Cikin Editocin LEADERSHIP A Yau, ni ne Shugaba Sam ya aike wa “Ok” ta karshe da hannunsa. Domin na yi aikin Jaridar Juma’a a ranar Alhamis da dare ya ba ni “Ok”, a ranar Juma’a da dare kuma ya mutu.
Hakika mun yi rashin shugaba mai girma.