Tare da Nasir S. Gwangwazo
Bisa la’akari da ɗimbin albarka da arzikin da Allah Ya yiwa Nijeriya ta kowacce fuska, za a iya cewa, ƙasa ce wacce ƙasashen duniya za su iya yin rububin zuwa, domin zuba hannun jari a cikinta.
Zuba hannun jari a ƙasa ya na taimakon ƙasar da a ka zuba ɗin, sannan a lokaci guda ya na kuma taimakon masu zuba hannun jarin, domin masu hikima sun a cewa, banza ba ta kai zomo kasuwa.
To, amma babban abin mamaki shi ne, har kawo yanzu Nijeriya ba samu masu zuba jari a cikinta ba yadda ya kamata, idan a ka yi la’akari da yawan albarkatunta. Haƙiƙa wannan babban abin dubawa ne, domin za a samu masu zuba jarin, tabbas da wasu daga cikin matsalolin ƙasar sun gushe.
Zuba hannun jari a ciki n ƙasa daga waje, ya na samar da aikin yi mai ɗimbin yawa ga marasa shi. Haka nan ya na kyautata rayuwar masu aikin yin su kansu. Bugu da ƙari kuma gwamnati da al’ummar ƙasa sun a ƙara samun kuɗaɗen shiga ta hanyoyi da dama sakamakon wannan zuba jari da a ka yi a cikin ƙasar.
Misali, a na shi ne, idan wani ƙasurgumin attajiri ko mutane su ka zo su ka buɗe kamfani a cikin ƙasar, dole za su ɗauki mutane aiki, za su biya haraji kuma za su sayi wasu kayayyakin a cikin ƙasar, wanda hakan ke nufin cewa, za su yiwa ’yan ƙasar ciniki kenan. Duka wannan samuwar arziki ga ƙasa da ’ya’yanta.
Nijeriya ta na da faɗin ƙasa, ta na da ma’adanai, ta na da yawan jama’a, ta na da yawan jama’a da za a iya ɗiba aiki, wanda hakan ke nuni da cewa, za a iya samun sauƙin kuɗin ƙwadago kenan na ma’aikata, haka nan akwai cinikayya a cikin ƙasar baya ga mutane masu ɗimbin basira da kuma matasa masu tarin yawa da haziƙai babu adadi.
Bugu da ƙari, Nijeriya ta na da ƙasar noma mai ingancin gaske (Grade A), sannan kuma ta na da yanayi mai matuƙar kyawu da ya dace da kowacce irin shuka, kamar damina, zafi da sanyi. Dukkanninsu su na dacewa da yanayin shuke-shuke daban-daban na tsirrai, waɗanda garaɓasa ce mai yawan ga duk wanda ya zo ya zuba jari a cikin ƙasar.
Akwai lokacin da mu ka hadu da wasu baƙin Turawa da su zo aiki Nijeriya su ke gaya ma na cewa, sun yi matuƙar mamaki da su ka ga yadda Nijeriya ta ke; su ka ce da a ce haka yanayin ƙasarsu yak e, lallai da sun fi kowa arziki a duniya, domin sun ga yadda yanayin daminarmu ya ke ba mai lalata shuka ba ne, kuma zafinmu da ranarmu masu amfani ne ga kimiyya da fasahar a wannan lokaci, hakazalika yanayin sanyinmu ma arziki ne mai yawa a cikinsa, idan da za a yi amfani da fasahar kimiyyar da ta kamata.
Wadannan Turawa sun gaya ma na cewa, babban abinda ya fi ba su mamaki a Nijeriya shi ne, duk da irin wannan yanayi mai albarka da mu ke da shi, amma a na iya ɗauke wuta a Nijeriya, domin ko su da ba su da irin albarkatu da Allah Ya jibge a ƙasar irin namu, ba su taɓa fuskantar wata matsala wacce ta shafi hasken wutar lantarki ba. Don haka su na matuƙar zumuɗi da shauƙin Nijeriya da su ga irin yadda albarka ke a cikin ƙasar.
To, amma duk da waɗannan alherai da Nijeriya ke danƙare a Nijeriya, ba a samun yawaitar masu zuba hannun jari a cikinta, waɗanda za su iya yin tasirin da ɗan ƙasa da gwamnati za su iya ji a jikinsu. Yawaicin waɗanda su ke iya zuba hannun jari a Nijeriya, masu zuƙe jinin ’yan ƙasar ne, kamar kamfanonin wayar sadarwa ko kuma a yanzu da a ke samun ’yan kasuwar ƙasar Chana da a ke zargi da bautar da mutanenmu a biranen kasuwanci irin su Kano a kasuwar Kantin Kwari.
To, gaskiyar magana ita ce, a yiwa Nijeriya tsarin da ire-iren masu zuba hannun jari na gaske za su samu ƙarfin gwiwar zuwa su zuba dukiyarsu a cikin ƙasar ba. Lallai akwai dalilai da dama kan haka, amma bari mu kawo abubuwa guda uku kacal, waɗanda su ne ginshiƙi!
Tsaro
Ingantaccen tsaro na daga cikin babban abinda ya ke sanyawa masu zuba jari su shigo cikin ƙasa su saki jiki su zuba dukiyarsu. Babu wanda zai so ya zuba dukiyarsa a wajen da za a iya sace shi rana tsaka ko a kawo hari yankin da dukiyar nan ta ke a lalata ta.
Babu wanda za sai so ya zuba dukiyarsa a garin da ya ke fargabar fita ya je wajen aiki, saboda rashin tabbas na ko zai dawo ko ba zai dawo ba. Haka kuma babu mai so ya zuba dukiyarsa a inda ɓarayi za su iya zuwa sace ma sa ko su yi ma sa fashi da makami su talauta shi.
A idanun wasu ƙasashen su na ganin cewa, babbar kasada ce shigowa cikin ƙasashe irin namu. Shi ya sa a ƙasashen Yamma a ke jinjinawa irin ƙungiyoyin nan masu zaman kansu da ke kawo agaji Nijeriya, kamar irin agajin rigakafin Poliyo da makamantansu, saboda tsananin yadda a ke kallon su a matsayin masu tarar aradu da ka.
Idan mu na son wannan matsala ta kau, sai shugabannin sun tabbatar tsaron rayuwa da dukiya a ƙasar, sannan kuma ’yan ƙasa su daina sata da fashi da makami!
Ayyuka
Gudanar da ayyuka da kuma samar da kayan more rayuwa na daga cikin manyan dalilan da su ka sa a ke ƙyamar zuwa a zuba a hannun jari a Nijeriya. Matuƙar babu hanyoyi masu kyau, babu wutar lantarki tsayayyiya, sannan babu ruwan famfo mai tsafta, zai yi wahala wani ya je ya zuba jarinsa a cikin ƙasar da ta ke fama da waɗannan matsaloli, domin rashin waɗannan abubuwa zai ƙara tsadar rayuwa da kashe kuɗi wajen gudanar da kamfani ko kasuwancin da a ka kafa.
Idan za ka kashe Naira 10 ka biya kuɗin wutar Nepa, sai ka kashe Naira 30 ko 40 wajen biyan kuɗin fetur ko dizel a janaretonka, baya ga kuɗin sayen shi kansa janareton, wanda tuni babu kasuwarsa a ƙas ashen duniya, saboda samuwar wutar lantarki a can ta sanya kasiwarsa ta mutu murus! Hatta a maƙotan ƙas ashe irin su Nijer ba a cinikin jenareto sai ta kama. Kai hatta kasuwar cocilan a duniya ta faɗi warwas! Kamfanonin da su ka rage su na ƙera su, su na ƙerawa ne saboda ƙas ashen marasa zuciya irin namu!
Idan a na so a zuba jari a Nijeriya, sai gwamnati ta tashi tsaye wajen gudanar da ayyuka, komai ya dawo daidai!
Nagarta
Nagarta wata aba ce wacce ba a ganinta a fili tan a tafiya ko a zaune ko a kishingiɗe, to amma tasirinta ya wuce na dalilai biyu da mu ka faɗa a baya. Rashin nagarta ne ya janyo matsalar tsaro a Nijeriya, domin da shugabanni sun yi nagarta su na bayar da kuɗin da a ke warewa fannin na tsaro, su kuma jami’an tsaro sun aiwatar da abinda ya kamata, sannan talakawan ƙasa ba su sata da fashi da makami, haƙiƙa da matsalar tsaro ba ta taso ba, ballantana har wani daga waje ya ji tsoron zuwa ya zuba hannun jari a cikin ƙasar.
Kazalika, da shugabanni bas a sace dukiyar ƙasa su na ɗurawa a aljihunsu, sun gudanar da ayyukan da su ka kamata a cikin ƙasar, tabbas da sai Nijeriya ta yi yanga kafin ta amince a zuba jari a cikin ƙasar tata.
Bugu da ƙari, babu wani mai zuba hannun jari da zai so ya yi mu’amula da mutumin da zai ha’ince shi. Don haka dole sai ma’aikata sun daina cin hanci da rashawa, su kuma jama’ar gari sai sun daina damfara da cuta ga baƙi masu zuba hannun jari, sannan wannan matsala ta rashin zuba hannun jari za ta kau!
Ya kamata mu sani cewa, banza ba ta kai zomo kasuwa! Idan har a na ganin ni’imomin da mu ke da su, amma a ka ƙi zuwa a zuba jari, to mu sani cewa, akwai dalili, kuma mu fara zargin kanmu, don mu gyara! Duk wanda ka ga ya zo ƙasarka ya zuba jari, to lallai ya san akwai mamora ne, amma ba zai zo ya zuba a banza da wofi ba!