An Bar Mata ‘Yan Siyasa A Baya –Fatima Bala

Daga Balarabe Abdullahi, Kaduna

An bayyana yadda manyan ‘yan siyasa ke jagorancin sanya mata a sahun baya, bayan zaɓe da cewar babbar matsala ce da ke addabar yadda mata ke da ƙudurin bayar da gudunmuwarsu da ta shafi siyasa a musamman in sun shiga takara a ko wane mataki na siyasa.

Wata fitacciyar ‘yar siyasa a jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa mai suna Hajiya Fati Bala Kankanba ta bayyana haka ga wakinmu a zantawr da ya yii  da ita kan  cikar Nujeriya  shekara 57 da samun ‘yanci.

Hajiya Fati Bala Kankanba ta ci gaba da cewar,tun da aka fara dimukuraɗ iyya a Nijeriya,mata na bayar da gagarumin gudunmuwa tun daga yaƙin neman zaɓe ya zuwa zaɓe,amma an fi son mata su zama ‘yan turin mota,bas u kasnce waɗ anda za su zama direbobi a motar siyasa ba.

Ta ƙara da cewar,a duk lokacin da aka kaɗ a kugen siyasa,ko da mata sun shiga tsakiyar fili,ƙiri-ƙiri ake mayar da su baya,domin wasu dalilai da ya shafi al’ada da kuma addini.Hakan bai dace ba,domin a halin yanzu mata na da ilimin da za su iya riƙe ko wane irin matsayi na siyasa,amma sai a ajiye su a gefe guda.

Duk da waɗ annan matsaloli da mata ke fuskanta,a cewar Hajiya Fati Bala Kankanba,ta ce mata ‘yan siyasa za su yi fitowar murucin kan dutse, na yadda za su shiga takara a matakai da dama,kuma tsarin da matan za su yi, Hajiya Fati ta ce za su sami nasara da yaddar mai duka.

Ta tunatar da al’ummar Nijeriya cewar,mata na da tausayi,gas u kuma da riƙe amanar duk wani abu da aka danƙa masu,wannan ne zai sa as sami shugabanci nagari da kowa zai murna da shi

Hajiya Fati Bala Kankanba ta kammala da yin kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yin addu’o’I ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, domin ya sami damar aiwatar da ayyukan da za su bunƙasa Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya.

Exit mobile version