Daga A.A Masagala Benin
A cikin wata hira da wakilinmu na Bennin a Jihar Edo ya yi da shugaban al’ummar Arewa mazuna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh, shugaban ya nuna godiyarsa da kuma jinjina ga rundunar soja ta kasa a kan kokarin da take yi na ganin kasarmu tana ci gaba da zama kasa guda al’umma daya, tare da jaddada kira ga ‘yan Arewa mazuna Kudoncin da su kwantar da hankalinsu su zauna lafiya tare da kusanta kansu ga gwamnati da shugabanninsu.
Alhaji Badamasi ya nuna bukatar da ke akwai na ’yan Arewa mazuna Kudu maso-gabas da su kasance cikin natsuwa kuma guje wa yayata labarin abin da bai faru ba domin hukuma da kafafen yada labarai ne suke da hurumin bayar da labarin abin da kasa take ci.
Kazalika, ya ce abu ne mai muhimmanci ga shugabannin ‘yan Arewa su rika fahimtar da jama’arsu muhimmancin kusantar gwamnati tare da wanzar da zaman lafiya. Ta bakinsa, “Ina bai wa jagororin al’umman Arewa na nan Kudonci da su rika shirya tarurrukan neman hadin kai da zaman lafiya, ina ganin idon ana haka za a iya warware kowace irin matsala domin da ‘yan Arewa da ‘yan Kudu duk ‘yan uwan juna muke.
A karshe, Alhaji Badamasi ya nunar cewa su shugabannin ‘yan Arewa mazauna Kudoncin kasar nan dawainiyarsu ce ci gaba da fadakarwa da kuma wayar da kan jama’arsu lokaci-lokaci domin cimma zaman lumana.