Zubairu M Lawal" />

Barace -Barace Na Jawo Wa Yan Arewa kasakanci A Nijeriya- Alhaji Adamu

Alhaji Usman Adamu (Doya 50) mazaunin garin Agyaragu dake karamar Hukumar Obi ta jihar Nasarawa yayi kira ga mahukunta dasu zage dantse wajen kawo karshen barace- barace a kasar nan.

Ya bayyana cewar yanzu zamani ya canza don haka bara ba addini bace. Kowa ya san idan ana maganar masu kudi a Nijeriya za’ace yan Arewa. Idan ana maganar abinci a Nijeriya za’ace yana Arewa. To me yasa talauchi da kaskanci dukl suke Arewa?.
Ya yi karin haske cewar ya goyi bayan Gwamnoni kuma yana kira ga Gwamnatin tarayya ta shiga cikin wanan maganar , bai kamata ace wanda ya haifi yaro,,har wai ace kulawa da shi ta gagari shi mahaiofin ba.
Bugu dakari kuma Gwamnati tayi doka mai karfi a tsarin karatun allo ko wanne yaro ya tsaya yayi karatun allo a jihar shi. A jihar shi a karamar Hukumar shi. karamar Hukumar shi kuma a garin shi.
Kada wani ya shiga wata jihar , sai idan yaro ya girma ya kai munzalin zuwa wani ga domin kan shi, ba wai iyayen shi su dauke shi daga wata jiha zuwa wata jiha ba.
Yara yi bayanin cewar kaskantar da addini ne ace yaro yazo karatun addini amma yana cikin kuncin rayuwa. Suma Malamai masu maganar cewa abinda gwamnati tayi bai da ce ba , ai basu kai ya’yan su karatu a wani gari ba.
Ya kara da yin haske cewar” alumman kudanchi suna sukar yan Arewa da cewar almajirai saboda ganin yadda yaranmu suke ,an kwashi yara daga Arewa an kai su kudu , to ana karatun allo a kudu ne?”
“Dan haka nake kira ga da gwamnonin Arewa su zage damtse wajen daukar wanan matakin . Gwamnonin Pilato da kuma Benuwe duk su shigo a hada karfi ayi dokar kowa ya ajiye yaran shi a garinsu suyi karatu . idan aka kama yaro  karami a wata Jihar da iyayen su suke a hukunta su.
Tun da farko ya fara magana ne akan rage yawan jam’iyyun siyasa da ake dasu a Nijeriya . yace ; jam’iyyun sunyi yawa . kamata yayi a rage su koma kamar biyar.
Saboda ragewar shine zai gyara tsarin siyasa, ba za a rika samun yan takara masu yawa ba. Yace yawan jam’iyyun da suka kai har tamanin da wani abu.
Ya kan sa yan siyasa suna amfani da sauran jam’iyyun wajen ganin sun tsayar da wanda suke so koda da karfi ya cizabe yace; a mai da jam’iyyun su koma kamar biyar , sanan a yiwa jam’iyyu masu zaman kansu rijista .
Kuma jam’iyyu masu zaman kansu a aikin su ya tsaya a karamar Hukumar da Jihar kada a yi amfani dashi a tarayya.
Mutum yana iya tsayawa takara a jam’iyya mai zaman kanta a zaben kansila ko Shugaban karamar Hukuma, ko dan majalisar dokoki ta jihar, ko kuma gwamna amma ban da dan majalisun tarayya da Dattawa ko Shugaban kasa .
Wanan sai jam’iyya mai ridista. Kuma idan aka rage jam’iyyu zai ba mutani damar fita suna kada kuri’u saboda yan takarar a kuma san yawan su.
Ya kara bayanin cewar bai kamata ace a Nijeriya yanzu ana amfani da tsarin masu zaben yan takara a zaben fidda gwani ba (Dalget ).
Saboda tsarin daliget shine yake jefa alumman kananan waholli . ana amfani dasu mutum, koda ba na kirki bane ya san, ko su nawa ne da kuma yawan kudaden da zai z yi amfani da su. Su kuma su zabe shi daga baya alumma su fada cikin da na sani.
Daga karshe ya bayyana cewar a dawo tsarin yar tinke tun daga gunduma zuwa karamar Hukumar zuwa ,Jihar zuwa tarayya idan alumma suna son mutum su zabe shi , idan aka yi hakan zamu rika samun Shugabanni na kirki.

Exit mobile version