Lafia, " />

Barace-barace Na Jawo Wa ’Yan Arewa Kasakanci – Alhaji Adamu

Alhaji Usman Adamu (Doya 50) mazaunin garin Agyaragu dake karamar Hukumar Obi ta jihar Nasarawa ya yi kira ga mahukunta da su zage dantse wajen kawo karshen barace-barace a Nijeriya.

Ya bayyana cewar, “yanzu zamani ya canza, don haka bara ba addini ba ce. Kowa ya san idan a na maganar masu kudi a Nijeriya za a ce ‘yan Arewa. Idan ana maganar abinci a Nijeriya za a ce ya na Arewa. To me ya sa talauci da kaskanci  dukl su ke Arewa?”

Ya yi karin haske cewar ya goyi bayan gwamnoni kuma ya na kira ga Gwamnatin Tarayya ta shiga cikin wanan maganar, bai kamata a ce wanda ya haifi yaro, har wai a ce kulawa da shi ta gagari shi mahaifin ba.

Bugu dakari kuma, gwamnati ta yi doka mai karfi a tsarin karatun allo ko wanne yaro ya tsaya ya yi karatun allo a jihar shi. A jihar shi a karamar Hukumar shi. Karamar Hukumar shi  kuma a garin shi.

Kada wani ya shiga wata jihar , sai idan yaro ya girma ya kai munzalin zuwa wani ga  domin kan shi, ba wai iyayen shi su dauke shi daga wata jiha zuwa  wata jiha ba.

Ya kara yin bayanin cewar kaskantar da addini ne ace yaro yazo karatun addini amma yana cikin kuncin rayuwa. Su ma Malamai masu maganar cewa abinda gwamnati ta yi bai da ce ba , ai ba su kai ‘ya’yan su karatu a wani gari ba.

Ya kara da yin haske  cewar, “al’umman kudanchi suna sukar ‘yan Arewa da cewar almajirai saboda ganin yadda yaranmu suke ,an kwashi yara daga Arewa an kai su kudu , to ana karatun allo a kudu ne?

“Dan haka na ke kira ga da gwamnonin Arewa su zage damtse wajen daukar wanan matakin . Gwamnonin Pilato da kuma Benuwe duk su shigo a hada karfi ayi dokar kowa ya ajiye yaran shi a garinsu suyi karatu. Idan a ka kama yaro  karami a wata Jihar da iyayen su su ke a hukunta su.”

Tun da farko ya fara magana ne akan rage yawan jam’iyyun siyasa da a ke da su a Nijeriya, ya ce, jam’iyyun sun yi yawa, kamata ya yi a rage su koma kamar biyar.

Saboda ragewar shi ne zai gyara tsarin siyasa, ba za a rika samun yan takara masu yawa ba. Ya ce, yawan jam’iyyun da suka kai har tamanin da wani abu.

Ya kan sa yan siyasa suna amfani da sauran jam’iyyun wajen ganin sun tsayar da wanda su ke so koda da karfi ya cizabe  yace; a mai da jam’iyyun su koma kamar biyar, sannan a yi wa jam’iyyu masu zaman kansu rijista.

Kuma jam’iyyu masu zaman kansu a aikin su ya tsaya a karamar Hukumar da Jihar kada a yi amfani dashi a tarayya.

Mutum ya na iya tsayawa takara a jam’iyya mai zaman kanta a zaben kansila ko Shugaban karamar Hukuma, ko dan majalisar dokoki ta jihar, ko  kuma gwamna amma ban da  dan majalisun tarayya da Dattawa ko Shugaban kasa.

Wannan sai jam’iyya mai ridista. Kuma idan aka rage jam’iyyu zai ba mutani damar fita suna kada kuri’u saboda yan takarar a kuma san yawan su.

Ya kara  bayanin cewar bai kamata ace a Nijeriya yanzu ana amfani da tsarin masu zaben ‘yan takara a zaben fidda gwani ba (deliget).

Saboda tsarin daliget shi ne ya ke jefa al’umman kananan wahalhalu a na amfani da su mutum, koda ba na kirki bane ya san, ko su nawa ne da kuma yawan kudaden da zai yi amfani da su. Su kuma su zabe shi daga baya al’umma su fada cikin da na sani.

Daga karshe ya bayyana cewar a dawo tsarin ’yar tinke tun daga gunduma zuwa karamar Hukumar zuwa Jihar zuwa tarayya idan al’umma su na son mutum su zabe shi, idan a ka yi hakan zamu rika samun shugabanni na kirki.

Exit mobile version