Daga Umar Faruk, Birnin kebbi
A cikin wannan makon da muke ciki ne mutane da ‘yan sanda suka kama wani barawon mota, wadda ya yi kokarin sace wata mota kirar Honda Academy da ke ajiye a gaban Ecobank a cikin garin Birnin-Kebbi. A cewar Alhaji Abubakar Zailani wanda shedan gani da ido ne, barawon ya bude motar kenan ya na kokarin tayar da ita sai mutane suka ankara, daga sai ya zuba da gudu cikin motar da ya sata in da mutane suka yi amfani da motocinsu wajen binsa a cikin Birnin-Bebbi. Ya yi ta zagaye a gari, amma a lokacin da ya iso dai dai kewayen Rima, sai ‘yan sanda suka kama shi tare da taimakon wasu mutane da suka biyo shi gaba daya, bayan kama shi mutane sun bashi kashi na fitar hankali da kayr ‘yan sanda da wasu mutane suka kubuttar das hi daga halaka sannan suka kai shi asibitin Sarki Yahaya da ke cikin garin Birnin- Bebbi domin duba lafiyar sa. Alhaji Zailani ya kara da cewa barawon motar su biyu ne, amma daya ya tsere, yayin da ya ga abin da ke faruwa.
Lamarin satar ababen hawa ya zama abin damuwa da tashin hankali, kuma ya zama a bin tsoro da damuwa ga ‘yan jihar Kebbi, duk kokarin da ‘ yan sandan Jihar yi wajen magance, in ji wani da shaida abin da ya faru.
Da ya ke zantawa da maikata asibitin, barawon ya shaida musu cewasunansa Isah Suleiman daga Samarun Zariya ta jihar Kaduna, kuma “ya zo jihar Kebbi ne da manufar sace mota”.