Daga Idris Umar, Zariya
A cikin makon da ya gabata ne wasu gungun barayi dauke da muggan makamai suka fado karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane da dama tare da kwasar dukiyar miliyoyin Naira.
Jaridar Leadershp A Yau ta ziyarci wanna garin Sabuwa shalkwatar karamar hukumar don ji da kuma ganin abin da ke faruwa, kasancewar manyan dazukan da ke yankin ya sa da yawan marasa gaskiya suka mamaye wannan yankunan tare da maida dazukan dandalin aikata ta’asarsu, domin kuwa duk mai tafiya in har ya biyo ta dajin Dogon Dawa ko dajin Birnin Gwari wanda duk wannan karamar hukumar ta yi mahada dasu, to sai jikinsa ya yi sanyi saboda hadarin da wajan ke ciki na matsalar gungun ‘yan fashi da makami da makami.
Bisa la’akari da hakan ne ma gwamnatin jihar Zamfara da ta jihar Katsina suka yi zaman sulhu da duk wani barawo da yake a wannan yankin domin kawo karshen firgicin da jama’ar yankin suke ciki tare da guje wa kashe rayuka da ake yi kullum a wadannan yankuna.
An kwashi tsawon watanni babu maganar tare hanya ko dirarwa kauyuka da barayi ke yi ko kwace shanun filani ko buge mai babur.
kwace babur, duk wannan ya zama tarihi a watannin da suka gabata, bayan zaman sulhu da gwamnati ta yi da wadanda suke aikata laifin.
Jaridar Leadership A Yau ta shiga wasu kauyakun da ke wannan yankin kamar Tashar Labo, inda ta sami labari barayin sun yi wa wani basarake Alhaji Ibrahim Garkuwan Kogo Hakimin Katsina, ruwan harsasai shi da wani dan’uwansa, Alhaji Kasimu, dukkansu suna asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya, a kwance bayan dukiyarsu da barayin su ka yi awan gaba dasu. Jaridar Leadership A Yau bata tsaya a wannan kauyen ba, ta leka wani kauye da ake kira Hayin Damo inda nanma barayin sun harbe wani dattijo mai suna Malam Umaru dan shekara sittin da haihuwa sannan
suka harbe dansa har lahira mai suna Malam Isa Umar dan shekara arba’in da biyar, kuma sun kashe su ne bisa zargin cewa sun sayar da shanu guda biyu alhalin ba shanunsu ba ne, hakan yasa ba su sami kudi ba.
Unguwar dan Kolo da Unguwar Tashar-bawa da Unguwar Madaci kuwa nan an yi batakashi ne da barayin da mutanen unguwar, inda binciken da Leadership Ayau ya nuna cewa, akasarin mutanen da ke wadannan unguwannin sun yi biyayya ga tsarin da gwamnati ta bayar na aje makamai da tabbatar da zaman lafiya wanda wasu da ake zargin sun fito daga dajin Dogon Dawa su kuma basu yarda da wancan sulhunba, hakan ya sa suka yi alwashin sai sun kauda duk wani barawo da ya ce ya tuba, kuma sun yi nasarar kashe mutum uka a wannan yankin da alwashin
Cewa, zasu dawo nan gaba don cigaba da nuna adawar su da tsarin da gwamnati ta kawo na sulhu.
A wata anguwa kuma mai iyaka tsakanin karamar hukumar Sabuwa da karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna su kuma da barayin suka dira a wani gida sai su ka yi rashin sa’a mai gidan baya nan, to a nan take suka dauke matar mai gidan sukayi garkuwa da ita har ya zuwa hada wannan rahoto babu labarin ta, kwanakin baya sun yi garkuwa da dan sarkin garin Kayawa Alhaji Hudu Muhammadu mai suna Sagir Hudu Muhamma dan shekara goma sha tara da ke kan hanyar garin na Sabuwa zuwa garin Yakawada ta karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, inda suka bukaci makudan kudade baya ga dukan kawo wuka da sukayi wa sarkin kafin suka sako yaron.
Jaridar Leadership A Yau ta yi kokarin jin ta bakin jami’in ‘yansanda na yankin D.P.O in da ya tabbatar da cewa, abubuwa sun faru amma dai ba shi da hurumin cewa, komai sai ya samu umurni daga shugabansa, amma dai a halin yanzu suna ci gaba da bincike.