Wani mai mota kirar ‘Mercedes Benz C-class’ mai duhu a launi ya yi mamakin ganin yadda aka yi wa motarsa da safe a bakin kofar gidansa, inda aka sace komai na motar sai kangarwar karfen kawai aka bari, bayan wasu gungun kwararrun barayi sun zayarci gidan tasa da daddare.
Lokacin da Paul Hampton mai shekaru 56, na garin West Bromwich, a kasar Burtaniya, ya ga makwabcinsa yana tsaye a gaban gidansa da safiyar ranar Alhamis, yaji a jikinsa cewa lallai wani abu ya faru da ba daidai ba, amma bai taba tunanin ceaw abin ya yi muni ba. Ya shan faka motarsa, wanda kudin ta ya kai dala miliyan £28,000, kirar Mercedes C-class, a wajen gidansu da ke layin Marsh, amma babu abin da ya taba faruwa a wannan ranar da misalin karfe 9:30 na dare. Da karfe 4:30 na safe, makwabcin nasu ya fara buga ma shi kofa yana ihun cewa ya fito ya ga motarsa, ko kuma abin da ya rage daga gare ta.
An kira jami’an bincike don daukar kwafin tambarin yatsun barayin daga motar da a ka sace, amma sun gaya wa Hamptons cewa ba za a iya samun dukkanin abubuwa da aka sace ba. Har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma Paul da kansa yace zai ba da kudi dala £1,000 ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga gurfanar da barayin.
“Lokacin da na fita kofar gidan da safe, na kasa gaskata abin da na gani. Ba su lalata kowane bangare na karfen motar ba, kawai an tsiraita motar ne. Wadannan kwararrun barayi ne da suka san mai suke yi, domin kowane dayansu yana da aikinsa. Ba su datse wayoyin a kokofin motar ba, sun kwance mahadan ne don kaucewa lalata shi, inda suka komai daki-daki,” in ji shi.