Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja
Sakamakon yunkurin da gwamnatin Jihar Neja ta fara na yashe madatsar ruwanta, wasu jihohi da ke makwabtaka da Kogin Neja na fuskantar barazana mai karfi ta ambaliyan ruwa. Jihohin sun hada da na Kebbi, Neja, Kogi, Anambra, Delta, Imo, Ribas da Bayelsa.
Wannan ambaliya da ke barazana, wacce masana ke hasashen ta zarce wacce aka yi fama da ita a shekarar 2012, ta dau hankali ne bayan da Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa Ta Kasa (NEMA) ta samu sakon gargadi daga jihar ta Neja. Wannan gargadi ya bayyana cewa madatsun ruwan Kainji Dam, Jebba Dam da Shiroro Dam sun cika fal! Kuma ba zasu iya cigaba da rike ruwan da ke cikinsu ba.
Wannan gargadi ne ya sanya Hukumar NEMA, a jiya Laraba ta fidda sanarwa mai kumshe da gargadi ga jihohin da aka lissafa, inda ta bukaci dasu kwashe mutane, don tseratar da rayukan al’ummarsu.
“A yanzun kuma mun sake samun wani gargadi na barazana daga cibiyar kula da kogin Neja wanda kuma hukumar NIHSA ta tabbatar da cewa madatsun ruwa sun cika tun kwanaki bakwai da suka wuce.
“A dalilin haka Hukumar NEMA take sanar da al’umma, musamman wadanda ke makwabtaka da Kogin Neja, ciki hard a mutanen jihohin Kebbi, Neja, Kogi, Anambra, Delta, Imo, Ribas da Bayelsa sun fi kowa fuskantar wannan barazana ta ambaliya nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.” In ji shi.