Sulaiman Ibrahim">

Barazanar Amfani Da Guba: Kotu Ta Raba Auren Shekara 10 A Ibadan

Wata kotu da ke Mapo a garin Ibadan a ranar Litinin ta raba auren shekaru 10 tsakanin wani dan acaba, Akinola Olaogun da matarsa, Shakirat, kan barazanar yi mata wanka da ruwan batir.

Da yake yanke hukunci, Cif Ademola Odunade, Shugaban kotun ya ce ya raba auren ne da nufin samun zaman lafiya.

Odunade ya ba da rikon yaransu guda biyu Ga ubansu Olaogun sannan na ukun kuma ya bai wa matar Shakirat.

Sannan mahaifin yaron zai dinga biyanta naira dubu 15,000 kowanne wata a matsayin kudin shayarwa.

Tun da farko, Olaogun, ya fada wa kotun cewa ya yi wa matarsa da ya rabu da ita barazanar yi mata wanka da ruwan batir saboda ta gudu tare da yaransu zuwa wajen masoyin nata.

Kuma Ya yarda ya bugi matar tasa.

”Mai girma mai sharia, gaskiya ne cewa nayi barazanar zuba ruwan batir akan Shakirat da mahaifiyarta. Amma Ba haka nake nufi ba, kawai ina so in ba ta tsoro ne, ”inji shi.

Tun da farko, Shakirat, wacce ke zaune a makarantar Owode-Academy ta bukaci kotun da ta ba ta takardar saki.

“Ya doke ni ya kuma yi min barazanar wanka da ruwan batir ni da mahaifiyata, ya kuma kwashe min kudi a inda nake boyewa.” In ji ta.

Exit mobile version