Duk da barazaranar masu kai har-hare, Shugaban Jami’ar Maiduguri Farfesa Ibrahim Njodi ya ce suna tare da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) game da neman danyen mai da ake yi a tafkin Chadi bayan harin da masu tada kayar baya suka kai makon da ya gabata.
Farfesa Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin da Karamin Ministan Man Fetur din kasar Dokta Ibe Kachikwu da kuma wasu manyan jami’an NNPC suka kai masa ziyara a karshen makon jiya.