Barazanar Safarar Bil’adama A Nijeriya…

Safarar Bil’adama

Daga Abdulrazak Yahuza Jere,

Ga dukkan alamu har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da matsalar da ake fama da ita ta safarar bil’adama a Nijeriya, sakamakon yadda masu ruwa da tsaki a yaki da abin ke kokarin nusar da mutane irin sabbin dabarun da masu wannan muguwar sana’a ke amfani da su wajen yaudarar wadanda suka fada a komarsu.

A wani bangare na kara karfafa yaki da safarar ta bil’adama, an shirya wani taron horaswa na yini uku a karshen makon da ya gabata domin kara wa mahalartan ilimi game da sabbin salon da masu safarar ke amfani da shi a wannan zamanin da nufin fadakar da al’umma da kuma ankarar da masu ruwa da tsaki a fannin yaki da matsalar.

Taron wanda ya gudana a Keffi da ke Jihar Nasarawa, an shirya ne bisa hadin gwiwa a tsakanin Hukumar Yaki Da Safarar Bil’adama ta Nijeriya (NAPTIP) da Kungiyar Tarayyar Turai (EU), da Gidauniyar Hadin Kan Hukumomi Bisa Kudirin Ci Gaban Duniya ta FIIAPP a karkashin Kungiyar Yaki Da Safarar Bil’adama Da Fasa Kwaurin Mutane (A-TIPSOM).

Horaswar wacce ta kunshi gabatar da kasidu da makaloli daga kwararru daban-daban, ta samu mahalarta daga kafafen yada labaru na jarida da rediyo da talabijin da shafukan sada zumunta da Sashen Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), da na Hukumar ‘Yansanda (NPF) da Gamayyar Kungiyoyin Yaki da Safarar Yara da Cin Zarafinsu (NACTAL) da kuma wasu jami’an NAPTIP.

Da yake gabatar da kasida mai taken “Bayani Game Da Safarar Bil’adama A Nijeriya”, Daraktan Tattara Bayanan Sirri da Horaswa da Samar da Ma’aikata na Hukumar NAPTIP, Mista Arinze Orakwue ya nunar da cewa yaki da safarar bil’adama ba na hukumarsu ce kawai ba, yaki ne na kowa da kowa musamman yadda lamarin ke kara sauya salo da kuma tagayyara wadanda suka auka ciki.

Kididdigar da aka bayyana a cikin bayanan ta nunar da cewa daga lokacin da aka tabbatar da kafuwar NAPTIP a 2003 zuwa yanzu, hukumar ta samu rahoton safar bil’adama sau dubu takwas da dari da talatin da biyu (8,132).

Sannan ta yi nasarar ceto mutanen da aka yaudare su suka auka komar masu safarar su dubu doma shashida da dari daya1(6,100). Bugu da kari, kididdigar ta ce hukumar ta samu nasarar gurfanar da wadanda aka kama da laifi su dari hudu da tamanin (480) inda aka yanke musu hukunci daban-daban.

Wakazalika, kamar yadda kididdigar ta nunar, akwai mutum sama da miliyan 32 da aka yi safarar su a fadin duniya bakidaya wadanda suka tsinci kansu a cikin tasku daban-daban.

Ita dai wannan muguwar sana’a kamar yadda kwararru a taron suka ayyana, tana samar wa masu yin ta da ribar akalla Dala Biliyan 150, wannan ma daga bayanan da Kungiyar ILO ta duniya ce ta fitar a shekarar 2014.

Kididdigar ta kuma bayyana cewa a yankin Kalifoniya na Kasar Amurka masu safarar bil’adama suna cin karensu babu babbaka, saboda suna tsunduma wadanda suka yi safara cikin karuwancin da ake biyan akalla Dala 100 (kimanin Naira dubu hamsin da shida 56,000) a kowace saduwa. Inda a rana ake tilasta wa mace ta yi lalata da mutum akalla shida zuwa tara. A wasu kasashen kuma, akwai inda ake tilasta wa ‘yan matan saduwa da maza sama da mutum 25 a duk yini.

Wannan ya sa muguwar sana’ar ta zama ta biyu a cikin miyagun harkallolin da ke kawo kudi a duniya baya ga safarar kwaya da makamai da suka kasance a kan gaba a duniya.

Da yake karin haske, Mista Arinze ya ce dalilan da suke sa a yi safar bil’adama a duniya su ne, “tsunduma wadanda aka yi safara a karuwanci, tilasta musu yin auren dole, amfani da su wurin barace-barace, tsunduma su a aikin karfi, safarar su domin a sayar da wasu sassan jikinsu ko a yi tsaface-tsaface da su.

“Masu safarar suna amfani da hanyoyi na yaudara sosai wajen rudin wadanda suke safara, ba za su taba yarda mutum ya gane cewa yaudarar sa suke yi ba. Makaryata ne da suke yin alkawarin karya, wasu kuma ana hada baki da danginsu ne na kusa a yi safararsu, wasu kuma sukan tsinci kansu a hannun wadannan miyagu ne sakamakon hadama da son banza. Don haka ya kamata mutane su farga da wadannan miyagu.

“Hanyoyin da masu safarar suka fi amfani da su wajen safarar mutane a nan Nijeriya su ne idan suka samo mutane, sai su bi da su ta wasu kasashen Afirka zuwa Turai. Sun fi fita da mutanen da za su yi safara ta kasar Benin, kasar ita ce babbar kofarsu, sai kuma Togo, Mali, Burkina-Faso, Libiya da sauransu. Tsarin yadda suke yaudarar shi ne da farko za su yaudari wadanda za a yi safarar su har su gamsu su amince za su bi su. Sai su yi safarar su daga gida zuwa kasar da suke son kai su, daga nan sai su cutar da su ko su rika amfani da su ta hanyar da suke so.” Ya bayyana.

Da yake magana a kan abubuwan da suke ingiza wannan muguwar sana’a kuwa, Mista Arinze ya ce rashin katamaimiyar sana’a da samar da damammaki ga matasa ta fuskar tattalin arziki na daga ciki, ya kara da cewa, “akwai kuma rashin samun damar karatu ta yadda matasanmu za su samu ilimi kamar yadda ya kamata, da rashin sanin makircin masu safarar a tsakanin iyalan wadanda abin ke shafa, hadamar matasa na yi wa kitse kallin rogo a kasashen waje, da kurakuran da ake samu daga bangaren mahukunta na rikon sakainar kashi ga lamarin, da kuma rashin tsaurara doka a kan masu kitsawa da aikata muguwar sana’ar ta safarar bil’adama”.

Shi ma da yake gabatar da kasidarsa a kan hanyoyin da ‘yan jarida za su bi wajen binciko aika-aikar masu safarar bil’adama, Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ACI Amos Okpu, ya yi kiran kara hadin gwiwa a tsakanin duk hukumomin da suke da rawar takawa kan yaki da safarar bil’adama tare da ‘yan jarida, domin a cewarsa, miyagun da ke sana’ar suna da tsari na fitar hankali.

Sauran wadanda suka gabatar da kasidu a kan ilmomi daban-daban da suka hada da Mista Olubiyi Olusayo, Mista Josiah Emerole da Mista Vincent Adekoye bakidaya sun nemi kowa da kowa ya mike haikan a kan wannan matsala domin miyagun na iya zama kusa da mutum su yi masa ill aba tare da ya sani ba.

A karshen taron dai an fitar da sanarwar manema labarai da ta bayyana cewa ya kamata kafafen yada labarai na Nijeriya su kara kaimi da kuma ankarewa wajen bayar da rahotannin ayyukan fataucin mutane da kara wayar da kan jama’a da kuma shigar da dukkanin kungiyoyin kafafen yada labarai cikin yakin.

Sannan a samu ingantacciyar aiwatar da dokar hana cin zarafi a kan mutane kamar yadda take kunshe a dokar (VAPP, Act, 2015), don kama masu wuraren da aka aikata laifin, da kuma yanke hukuncin da ya dace ga masu laifi, gami da masu ba da dama ga masu laifin suna cin karensu babu babbaka.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Hukumar NAPTIP na bukatar fadada rassanta ya zama tana da ofishi a dukkan Jihohin Tarayyar Nijeriya da dukkan kananan hukumomi 774. Haka nan ya kamata masu ruwa da tsaki su zagaya da ‘yan jarida rangadi a wasu kasashen da suke zuwa domin ganin halin da wadanda abin ya shafa ke ciki, kana su kara bayyana bala’in da wannan muguwar sana’a ke jefa mutane a ciki.

Wakazalika, an yi kira ga Hukumar NAPTIP da kafafen yada labarai da sauran hukumomin da abin ya shafa su yi kokarin bin diddigin kudaden da ake samu daga muguwar sana’ar ta safarar bil’adama (TIP). Kuma ana ana bukatar gwamnati ta samar da karin kudade na aiki ga NAPTIP domin ta samu sukunin aiwatar da shirye-shiryenta. Haka nan an bayyana cewa hukumar tana bukatar amfani da karin kwararrun masu ba da shawara da warware damuwa ga wadanda abin ya shafa, musamman kan abubuwan da suka shafi zamantakewa da tunani.

Sannan an bayyana cewa ya kamata masu ruwa da tsaki su bullo da hanyoyin da ‘yan jarida za su kara himma da samun horo kan sabbin abubuwan da suke kunno kai a muguwar sana’ar ta safarar bil’adama da fasa-kwaurin mutane.

Kana an nemi gwamnati ta bayar da dama ga jami’an hukumar ta NAPTIP su rika daukar makami saboda hadarin aikin da suke yi idan suka fuskanci masu safarar bil’adama.

 

Exit mobile version