Muhammad Maitela" />

Barazanar Tsaro Ba Ta Hana Borno Da Yobe Zabe Ba Amma Ta Hana Geidam Jefa Kuri’a

Duk da matsalar tsaro da kai hare-hare a wasu sassan jihohin Borno da Yobe, sa’o’i kadan kafin a fara gudanar da zaben shugaban kasa tare da na ’yan majalisun tarayya a wadannan jihohin hakan bai hana jama’a yin tururuwa zuwa rumfunan zabe ba, to amma gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Geidam, bai iya samun zarafin zuwa mazabarsa ya kada kuri’a ba, saboda mummunan harin da ya afku a yankin da jefa kuri’ar.
Rahotannin da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta tattaro daga jama’ar jihohin sun bayyana cewa, jama’a sun nuna halin ba gudu ba ja da baya wajen fita rumfunan zaben tare da jefa kuri’unsu, duk da wani harin da wasu mahara da a ke kyautata zaton ’yan Boko Haram ne su ka kai kauyen Zabarmari a karamar hukumar Jere da wasu unguwannin da ke babban birnin jihar Borno, wato Maiduguri.

Bugu da kari kuma, a makwabciyar jihar; wato jihar Yobe, wacce ita ma ta na fama da matsalar tsaro, can ma wasu maharan sun kai makamancin wannan harin a garin Gaidam ta jihar Yobe, amma bayanai sun nuna cewa, ba a fasa fita zaben ba.
A jihar Bornon, maharan sun farmaki kauyen, wanda ya ke daf da birnin Maiduguri mai tazarar kilomita 30 da kimanin karfe 6:30 na safe; awa guda da rabi kafin a fara zaben.
Alhaji Bakaka Modu, mazaunin kauyen, ya bayyana cewa, harin ya tilasta wa daruruwan jama’a kaurace wa kauyen zuwa birnin Maiduguri. Duk da ba a bayyana adadin wadanda su ka rasu ba a wannan harin, amma dai wasu majiyoyin da ba na jami’an tsaro ba sun bayyana cewa wasu sun mutu tare da samun raunukan mutane.
Amma wani mazaunin Borno, Alhaji Abubakar Gamandi Baga, ya shaida wa wakilinmu a jihar cewa, duk da wannan barazanar tsaron, bai sanyaya gwiwar jama’ar jihar fitowa rumfunan zaben ba domin su jefa kuri’unsu.
“Yanzu haka da na ke magana da kai, Ina rumfar zabe mai suna ‘Doro Polling Unit’ kuma mazabar cike ta ke da jama’a; kowa ya na kokarin jefa kuri’unsa. Duk da yadda a ke fama da barazanar tsaro a wasu sassa da unguwanni, amma dai jama’a su na harkar zaben,” in ji shi.
Alhaji Muhammed Shettima Kuburi Kukawa ya shaidar da cewa, zaben yau din ya samu tagomashi tare da fitowar jama’a zuwa mazabun domin gudanar da zaben. Wannan kuma, duk da barazanar kai hare-hare a birnin Maiduguri da wasu sassan jihar Borno.
“Yanzu ga shi mu na kan layi domin jefa kuri’unmu, kuma komai ya na tafiya a cikin tsari da tsanaki. Sannan kamar yadda mu ka yi magana da jama’a a rumfunan zaben daban-daban, jama’a su na cigaba da tururuwa zuwa gudanar da zabukansu.
“Kuma bisa gaskiya na dade rabon da na ga dandazon jama’a a rumfunan zabe irin wannan lokaci. Jama’a sun nuna gamsuwa tare da fahimtar cewa kuri’arsu ’yancinsu ce, kuma mu na fatan kammala wadannan zabuka lami lafiya.”
Haka ita ma Malama Falmata, wadda wakilinmu tarar a kan layin zaben a rumfar zabe ta Kofar Fada da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta shaida yadda ta gamsu da yadda zaben ke gudana tare da fitowar dandazon jama’a.
“Ina cikin murna da ganin fitowar jama’a fiye da kowanne lokaci, kuma yanzu haka a shirye na ke da na jefa kuri’ata.”
Malam Saleh Ali Gaidam ya shaida wa LEADERSHIP A YAU LAHADI cewa, duk da yunkurin da maharan kungiyar Boko Haram su ka yi (wato sau biyu a safiyar zaben) wajen kai hari a garin Gaidam a jihar ta Yobe, amma abin ya ci tura, inda sojojin Nijeriya su ka taka mu su birki.
“Wanda zancen da na ke yi da kai yanzu haka jama’a a garin su na cigaba da gudanar da sha’aninsu tare da dumfarar rumfunan zabe, domin gudanar da zaben,” ya tabbatar.
Dangane da wannan ne babban Daraktan yada labarai a ofishin gwamnan jihar Yobe, Malam Abdullahi Bego, ya bayyana cewa, bisa dalilin matsalar tsaron ne gwamnan jihar ba zai samu zarafin zuwa mazabarsa ta Bukarti da ke karamar hukumar Yunusari mai tazarar kilomita 230 daga Damaturu ba.
Ya ce, wannan ya zo ne ta dalilin wannan hari da mayakan su ka kai a garin Gaidam da sanyin safiyar ranar zaben, wanda daga bisani sojoji sun murkushe yunkurin maharan tare da kara kaimi wajen bai wa jama’a kariya.
Ya kara da cewa, hakan zai bai wa jami’an tsaron cikakkiyar damar karkata hankulansu zuwa ga bai wa jama’a tsaro maimakon raba hankalinsu zuwa gida biyu.
“Zuwan Gwamna Gaidam mazabarsa zai bukaci karin jami’an tsaro da yawa, wadanda za su raka shi zuwa yankin, kuma hakan zai tilasta jawo hankalin jami’an tsaro da dama da a ka tura a wasu sassan jihar.
“Kuma Gwamna ya dauki wannan matsaya ne bayan da ya tuntubi bangarorin tsaro da ke aiki a jihar. Bisa ga wannan kuma ya yaba matuka dangane da yadda jama’ar jihar su ka fito kwansu da kwarkwata zuwa rumfunan zabe domin jefa kuri’unsu.”
A dalilin matsalar tsaron, hukumar INEC a jihar Yobe ta canja rumfunan zaben karamar hukumar Gujba zuwa Damaturu, babban birnin jihar Yobe, lamarin da ya jawo shi ma dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, ya jefa kuri’arsa a mazabar ‘Phase One’ da ke Damaturun.

Exit mobile version