Barazanar ‘Yan Bindiga: Ku Ba Mu Naira Miliyan 24 Ko Mu Yi Muku Kisan Kare-dangi

Kisan

Daga Hussaini Yero,

Wasu gungun ‘yanta’adda da suka addabi jihar Zamfara, Sun bayyana cewa, dole a kai musu zunzurutun kudi naira miliyan ashirin da hudu, ko kuma mutanen wasu kauyuka guda ashirin da tara da ke karamar hukumar Bukkuyum su dandana kudarsu.

Gungun ‘yanta’addar sun rubuta wasika zuwa ga shugabannin al’ummar wannan yanki, wadda a cikinta suka bukaci kowane kauyr su hada musu,kudi daga naira dubu dari biyar zuwa naira miliyan biyar, ko su dandana kudarsu.

Rahotannin da suka fito daga wannan yanki sun nuna cewa, ‘yanta’addar sun yi barazanar cewa, za su yi wa mutanen wadannan kauyaku guda tara kisan kare dangi, maukar sun kasa biyan kudin fansar da suka yanke musu.

Mazauna wadannan kauyuka sun gaya wa ‘yanjarida cewa, yanzu haka, har sun fara hada wadannan kudi, don su biya su tsira da rayuwarsu.

‘Yanta’addar dai sun aika wannan sako ne, ta bakin wadanda suka saki. Kauyukan da ‘yanta’adda suka bukaci su hada wannan kudi su ne, Yangalma da Tungar Gebe da Wawan Iccen Ibrahim da Wawan Iccen Salihu da Galle da Nannarki da Ruwan Kura da Gangara da kuma Gaude.

Exit mobile version