Barcelona Ba Ta Yi Nasara Ba A Wasanta Da Espanyol

Wu Lei na Espanyol ya haramta wa Barcelona cin wasan hamayyar La Liga na birnin Kataloniya bayan ya farke kwallo ta biyu a filin wasa na RCDE.

Masu masaukin bakin, wadanda su ne na karshe a teburin La Liga, sun zira kwallon farko ne ta kafar David Lopez, inda ya ci kwallon da ka.

Barcelona ta ja ragamar wasan sakamakon kwallayen da Luis Suarez da kuma Arturo Vidal suka ci, amma an kori Frenkie de Jong daga wasan saboda karbar katin gargadi sau biyu.

Suarez wanda zai cika shekara 33 da haihuwa a wannan watan, ya ci ko kuma ya taimaka an ci kwallo 10 na baya-bayan nan a Barcelona.

Wu Lei shi ne dan kasar China na farko da ya taba zira wa Barca kwallo a raga bayan da Matias Vargas ya ba shi ita – kwallonsa ta shida kenan a kakar bana.

Da wannan sakamakon, Barca ta hau saman Real Madrid a teburi – wadda ta lallasa Getafe 3-0 ranar Asabar – da tazarar kwallo biyu.

Espanyol wadda ta gaza cin wasan hamayyar a wasa 21 da ta buga da Barca, yanzu ta dan farfado in aka kwatanta da makonnin da suka wuce sakamakon sauyin koci da ta yi.

Abelardo ne sabon kocin da kungiyar ta dauka kuma na uku a wannan kakar – wannan ne wasansa na farko.

Exit mobile version