Barcelona Da Neymar Sun Sasanta

Neymar

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar ranar Litinin cewar ta sasanta da tsohon dan wasanta Neymar kan takkaddamar da ke tsakaninta da wasan tawagar Brazil din wanda a yanzu yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German.

Dan kwallon Brazil din da Barcelona sun samu takaddama a tsakaninsu, bayan da Barcelona ta sayar da Neymar ga Paris St-Germain a shekarar 2017, cinikin da har yanzu ba’ayi wanda ya fishi tsada ba a kwallon kafa.

Neymar ya yi zargin Barcelona ba ta biya shi alawus a kwantiragin da ya saka hannu a Oktoban shekara ta 2016 ba, kafin ya koma Paris St Germain kan Yuro miliyan 222 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Hakan ne ya sa dan wasan Brazil din ya kai Barcelona kara domin a biya shi Yuro miliyan 46.3, ita kuma kungiyar Barcelona ta yi karar shi da cewar ya karya ka’idar yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Wani alkali a Barcelona ya yanke hukuncin a cikin watan Yuni cewar Neymar ya biya kungiyar Camp Nou Yuro miliyan 6.7 amma wasu kafar yada labarai a Sifaniya sun ce Neymar ya daukaka kara ya kuma sake maka Barcelona a kotu kan wani zargin na da ban.

Barcelona ta sanar da cewar ta yi sulhu da Neymar, an kuma kawo karshen tuhume- tuhumen da ke tsakaninsu a kotu yanzu komai ya wuce sai dai har yanzu dan wasan bai ce komai ba game da lamarin.

Exit mobile version