Abba Ibrahim Wada" />

Barcelona Da PSG Su Na Zawarcin Ericksen Na Tottenham

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona bata hakura da zawarcin dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ba, Cristian Ericksen dan kasar Denmark.
A kakar wasan data gabata ne kungiyar Barcelona ta nemi dan wasan bayan data siyar da Neymar zuwa PSG sai dai kungiyar ta buge da siyan Ousaman Dembele daga Dortmund sannan kuma a watan Janairu ta siyi Philipe Coutinho daga Liberpool
Ericksen dai tauraruwarsa tana haskawa a gasar firimiya a kungiyar ta Tottenham bayan da ya zura kwallaye goma sannan kuma ya taimaka aka zura kwallaye 9 acikin wasanni 36 daya bugawa kungiyar da suka hada dana firimiya da kuma na cin kofin zakarun turai.
Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Tottenham tana son karawa dan wasan kwantaragi domin idan ta tashi siyar dashi ta siyar dashi da tsada sakamakon shekaru biyu ya ragewa dan wasan a kungiyar.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta PSG tana zawarcin dan wasan wanda take ganin zai maye mata gurbin Marco Beratti wanda zai bar kungiyar a wannan lokacin zuwa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dake kasar Italiya.
Sai dai itama kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana zawarcin dan wasan bayan da ake zaton zata siyar da dan wasa Ander Herrera wanda zai koma PSG saboda United din taki kara nasa albashin da yake bukata.*

Exit mobile version