Abba Ibrahim Wada" />

Barcelona Na Zawarcin Lacazette Na Arsenal

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fara zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Aledandre Lacazette domin ya maye gurbin Suares a kakar wasa mai zuwa.
Tun a kwanakin baya aka fara dan ganta Barcelona da ‘yan wasan gaba masu zura kwallo a raga wadanda zasu maye mata gurbin Luis Suares wanda ake tunanin zai bar kungiyar zuwa kasar China a kakar wasa mai zuwa duk da cewa kociyan kungiyar ya bayyana cewa yanason dan wasan ya cigaba da zama.
Dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antoine Griezman, shine dan wasan da Barcelona ta bayyana tun a shekarun baya wanda zai maye gurbin Suares sai dai dan wasan yaki amincewa da komawa Barcelona kuma ya sake sabon kwantaragi da kungiyar.
Jaridu daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa dan wasa Aledandre Lacazette shine wanda kungiyar zata nema idan har Giezman ya sake zuba musu kasa a ido yace bazai koma kungiyar ba a kakar wasa mai zuwa.
Wakilin dan wasa Lacazette dai shine wakilin tsohon dan wasan Barcelona, Eric Abidal, wanda, kuma yanzu shine darakta a kungiyar, hakan yasa ake ganin idan Barcelona ta bayyana aniyarta na siyan dan wasan gaban bazai mata wahalar samu ba.
Sai dai abune mai wahala Arsenal ta amince ta siyar da dan wasan nata mai shekara 27 a duniya wanda ya zura kwallaye 18 a wannan kakar sai dai amma kuma idan har ta tabbata zata siyar dashi zata bukaci sama da fam miliyan 53 data biya kungiyar Lyon akan dan wasan a shekara ta 2017.

Exit mobile version