Barcelona Ta Dauki Emerson Royar Daga Real Betis

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dauki dan wasa na uku cikin mako daya, bayan da ta dauko mai tsaron baya, Emerson Royal daga kungiyar kwallon kaafa t Real Betis mai buga gasar La liga.

Tun farko dai Emerson, mai shekara 22 a duniya ya je kungiyar Barcelona daga kungiyar Brazil, Atletico Mineiro a watan Janairun shekara ta 2019 kan yarjejeniya uku da ta hada da Real Betis a ciki.

Hakan ne ya sa dan kwallon ya je ya buga wa Real Betis wasannin aro, yanzu kuma Barcelona za ta amfana da shi kamar yadda duka kungiyoyin biyu suka amince da tsarin tun farko.

Kuma Barcelona ta bukaci dan wasan na Brazil ya koma Camp Nou ne daga cikin kwantiragin da suka amince tun farko sannan tun farkon makon nan Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Sergio Aguero da kuma Eric Garcia dukkansu daga Manchester City.

Dan wasan Argentina, Aguero da na Sifaniya, Garcia, za su koma Camp Nou da zarar yarjejeniyarsu ta kare a karshen watan nan a Manchester City wadda tayi rashin nasara a wasan karshe na kofin zakarun turai a ranar Asabar din data gabata.

Haka kuma ana alakanta dan kwallon Liverpool, Georginio Wijnaldum da cewar zai koma Barcelona da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen watan nan a kungiyar ta kasar Ingila sannan bugu da kari Barcelona tana bibiyar dan wasa Memphi Depay, wanda shima kwantiraginsa zai kare a Lyon a karshen kakar bana.

Emerson ya buga wa Real Betis wasanni 79 kuma ya ci kwalllo biyar ya kuma bayar da 10 aka zura a raga sannan Emerson ya taka rawar gani a kakar da ta kare a Betis, wadda Manuel Pellegrini ke jan ragama da ta yi ta shida a La Liga da hakan ya sa za ta buga Europa League a badi.

Emerson ya wakilci tawagar ‘yan wasan kasar Brazil a wasannin matasa ‘yan kasa da shekara 20 da ta 23, ya kuma buga wa babbar kungiya wasan farko cikin watan Nuwambar shekara ta 2019.

Exit mobile version